Showing posts with label Hausa Stuff. Show all posts
Showing posts with label Hausa Stuff. Show all posts

Wadansu Yan Majalisar Wakilai 2 Sun Fice Daga Jam’iyyar APC

‘Yan majalisar wakilai biyu sun bayyana ficewar su daga jam’iyyar APC mai mulki da safiyar yau Laraba, daga cikin ‘yan majalisar ya koma jam’iyyar PDP, amma daya dan majalisar har zuwa yanzu bai bayyana wacce jam’iyya zai koma ba.
]‘Yan majalisar sun mika wasikun ficewarsu daga jam’iyyar ne ga shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, in da ya Dogaran ya karanta anniyar ‘yan majalisar a zauren majalisar wakilai.
Babatunde Kolawale wanda yake wakiltar mazabar Akoko ta arewa masu yamma dake jihar Ondo, a wasikar shi ya bayyana aniyar shi ta komawa jam’iyyar adawa ta PDP.
Munkaila Kazzim, mai wakiltar mazabar tarayyya ta Abeokuta ta arewa dake jihar Ogun, a tashi wasikar bai kai ga bayyana wacce jam’iyya zai koma ba.
Dukkan mutanen biyu sun bayyana rikita-rikitar zabukkan fidda gwani na jam’iyyar APC, a matsayin dalilin su na ficewa daga jam’iyyar, inda Mista Kazzim ya zargi jam’iyyar da siyasar ubangida, ta inda in baka da ubangida ba zaka samu tikitin tsayawa takara ba.

Rundunar Sojojin Jihar Zamfara Ta Yabawa `Yan Sa-kai Na Jihar

Heidikwatar rundunar sojojin Nijeriya ta yaba da dauka jami’an tsaro na farin kaya da gwamnatin jihar Zamfara ta dauka don tallafa wa kokarin da jami’an tsaro ke yi a fadin jihar don kawo karshen ‘yan ta’adda da suka addabi jama’a jihar.
Mukaddashin daraktan watsa labaran rundunar, Birgadiya janar John Ajim ya bayyana haka a garin Gusau babban birin jihar zamfara a lokacin da yake tattaunawa da yan jarida, ya ce, jami’an sojoji sun kasance a cikin wadanda suka tantance ‘yan sa kan ‘Cibilian JTF.
Ya bayyana cewa sojojin na nan a kan bakan sun a ci gaba da gudanar da shirin nan ‘Operation Sharan Daji’ don fatattakar ‘yan ta’adda a fadin jihar.
Agim ya kuma kara da cewa, shirin na ‘Operation Sharan Daji, OPSD’ ya samu karin karfin gwiwa daga hedikwatar rundunar tsaro ta kasa, ta haka suka samu nasarar kai samame a fadin jihar don fattakar ‘yan ta’addan a dazuzzukan da suke boye suna aikata mugun aikin nasu.
“harin da ake kai musu a kai kai ta sama ya ruda su a halin yanzu basa iya kai wani hari na azo a gani, a kullun suna kan gudu ne daga nan zuwa can don tsoro halin da za su shiga, inji shi.
Ya kuma kara da cewa, a tsakanin wannna lokacin da ake magana rundunar sojojin sun samu nasarar kwato shaye fiye da 1,444 da tumaki 478 da rakuma 11 da jakuna 14 da raguna 56 da kuma akuyoyi 293.
Janar Agim ya kuma kara da cewa, an kuma samu nasarar kwato bimdiga kirar AK 47 guda 24 da wasu bindiga guda 2 da kuma albarushai 40 da sauran muggan makamai daga hannun ‘yan ta’addan a samamen da sojojin ke kai wa yankin.
Ya kuma yaba da hadin kai da ake samu a tsakanin gwamnatin Nijeriya da na jumhoriyyar Nijar, musamman rndunar hadunb kai da aka kafa a watan Satumba na 2018.
Ya kuma kara da cewa, wannna hadin gwiwar ya haifar da basarar shiga dazuka dake bangaren kaar Nijar da suka hada ‘Sahiel forest’ da Gidan Jiya inda ‘yan ta’addan ke tsrewa in an kai musu hari bayan sun aikata mumunan aikin nasu.

Kalli Yadda Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Sojojin Najeriya Da Wasu Sojoji Da Dama A Maiduguri

Boko Haram Sun Kashe Kwamandan Sojojin Najeriya Da Wasu Sojoji Da Dama A Maiduguri
Wasu mayakan Boko Haram, sun yi wa sojojin Najeriya shahadar-kuda, inda suka afka musu bagatatan, har suka kashe kwamandan wani ayarin sojoji da kuma wasu sojojin da aka tabbatar da sun kai dozin da yawa.
Wata majiya ce daga cikin hukumomin tsaro na sojojin kasar nan ta sanar da manema labarai labarin wannan mummunan hari.
Majiyar ta kara da cewa maharan sun kuma tsere da dimbin muggan makamai da tulin albarusai a wannan hari da su ka kai wa Bataliya ta 157 da ke Metele, cikin Karamar Hukumar Abadam, jihar Barno.
Sun kai harin ne a ranar Lahadi da wajen karfe 6 na yamma.
Harin dai wani koma baya ne ga kokarin da sojojin Najeriya ke yi wajen ganin an fatattaki Boko Haram daga Arewa maso Gabacin kasar nan.
Akwai fargabar makomar sojojin da ke wannan sansani, wanda ko cikin wata daya da ya wuce sai da Boko Haram suka kai masa hari.
A yanzu kuma hukumar tsaro ta sojoji na ta kokarin shawo kan damuwar da harin ya haifar, ta hanyar shirin sabon harin kakkabe Boko Haram na game-gari, na musamman.
Wakilinmu ya gano cewa har zuwa Talata da safe ana ta kokarin tsinto gawarwakin sojojin Najeriya, ana kwashe su daga wurin da aka kai musu harin.
Sai dai kuma wannan majiyar ba ta iya fayyace yawan Boko Haram da aka kashe a wurin gumurzun ba.
Majiya ta ce wanda aka kashe din wani Laftanar Kanar ne, wanda ya dade ya na jagorantar ayarin rundunar.
An ce ya taba kin tattara sojoji su fita yaki da Boko Haram, yayin da shi kuma ya bayyana dalilin sa na rashin makamai marasa garambawul.
An dai ki bayyana sunan Laftanar Kanar din da aka kashe, saboda ba a san ko hukuma ba ta kai ga sanar da iyalan mamacin ba.
Idan ba a manta ba, Boko Haram sun kai wa wannan sansani mummunan hari, a ranar 8 Ga Oktoba, har suka kashe sojoji 18, suka ji wa wasu 8 raunuka. Jaridu sun ruwaito muku wancan hari da aka kai.
An kuma akalla sojoji 157 ne suka bace lokacin, kuma har ya zuwa yau sama da wata daya, hukum

Cardi b Bought Her Mama House(Video)


Cardi B, who found fame after she hit single 'Bodak Yellow' has bought her mother a two-story property and says it's a childhood dream come true.

The 'Invasion of Privacy' rapper shared videos on Instagram of the new home she purchased for her mother.

In the videos, the mother of one gave a tour of the well-furnished building, captioning the post 'Stay down till you come up! Its always been a dream to buy my mother a house,' began Cardi's caption.

She revealed in her first video that she has been wanting to buy her mom a home for some time. "Last year I was so thirsty to buy my mom a house but the ones I was interested in her weren’t at my price range. I worked and worked and now I’m here!!

'Thank you, everybody,, who supported me to make my childhood dreams come true! Buy my momma a house !!.....don’t ask me for shit motherf***kers I got big girls bills!'

Ahmad Musa Ya Kai Hukumar Kwallon Afrika Kara Kotu

Dan wasan Najeriya, Ahmed Musa ya bukaci Hukumar kwallon kafa ta Afrika da ta gudanar da bincike domin tantance sahihancin kwallaye 2 da Super Eagels ta Najeriya ta jefa a ragar Afrika ta Kudu amma alkalin wasa ya soke a karawar da suka yi a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika.
Alkalin wasan dan asalin Gambia, Bakary Gassama ya soke kwallayen da Kelechi Iheanacho da Ahmed Musan suka zura a ragar Afrika ta Kudu kuma babu wasu kwararan dalilan da suka saka ya hana kwallayen.
Koda yake alkalin ya amince da tafka kuskure , sannan kuma ya nemi afuwan Musa, in da ya ce, wani lokacin ana samun irin wannan kuskuren musamman saboda rashin na’urar taimaka wa alkalin wasa.
Tuni dai Najeriya ta samu nasarar samun tikitin halartar Gasar Cin Kofin Afrika .wanda za’ayi a kasar Kamaru a shekara mai zuwa duk da cewa ta tashi wasan ne 1-1 da Afrika ta Kudu a birnin Johannesburg.
Najeriya dai kawo yanzu tana matsayi na daya acikin rukunin da maki 11 sai kasar Afirka ta kudun a matsayi na biyu sai kuma kasar Libya a matsayi na uku yayinda kasar Sychelles take a matsayi na hudu kuma na karsh
#Hausaleadership

Shin Ko Real Madrid Tana Neman Sayan Neymar Ne?

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta musanta batun da ke cewa tana shirye-shiryen siyan dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG kuma mafi tsada a duniya wato Neymar Junior a kakar wasa mai zuwa.
Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce babu wani shiri a kasa game da tunanin siyo dan wasan wanda PSG ta siyo daga Barcelona kakar da ta gabata kan kudi yuro miliyan 200 kuma hakan yasa ya fi kowanne dan wasa tsada a duniya.
Haka zalika, Real Madrid ta ce bata yi wata Magana da dan wasan ko kuma kungiyar tasa ta PSG ba kawo yanzu sai dai bata fitar da ran cewa ba za ta siyi dan wasan ba a nan gaba idan ta samu damar yin hakan.
Wata kafar yada labarai a Sipaniya dai ta yi ikirarin cewa, Real Madrid din na gab da siyan dan wasa Neymar kan Yuro miliyan 310 kudi mafi yawa da wata kungiya ta taba taya dan wasa a tarihin cinikayyar ‘yan wasa.
Kawo yanzu dai Neymar ya zura a kalla kwallaye 28 a wasanni 30 kacal da ya bugawa PSG tun bayan komawarsa sakamakon jinyar da ya yi ta fama da ita a kakar wasannin da ta gabata. Kungiyar kwallon kafa ta PSG dai ta bayyana cewa ba za ta siyar da dan wasan ba kuma duk kungiyar da takeson siyan dan wasan ba za ta samu siyansa ba.
Real Madrid dai har yanzu bata maye gurbin Ronaldo bat un bayan da ta siyar dashi zuwa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus dake kasar Italiya kuma kawo yanzu tauraruwar dan wasan tana haska wa a kasar Italiya.
#Leadrshipayau

Buhari Ya ce ‘Yan Najeriya Su Yi koyi Da Jonathan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar su yi koyi da halaye irin na tsaohon shugaban kasar Goodluck Jonathan.
“Shugaba Buhari ya yi amannar cewa irin rayuwar da tsohon shugaban ya gudanar abar koyi ce ga dukkan matasan kasar,” in ji sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Mr Femi Adesina ya fitar.
Ya fitar da sanarwar ce domin taya tsohon shugaban murnar cika shekara 61 a duniya.
Shugaba Buhari ya kara da cewa rayuwar Goodluck Jonathan ta zama izina ga “dukkan mutumin da ke son ya yi koyi, ya yi aiki tukuru sannan ya sanya hannu wajen gina kasa ta gari.”
Ya taya tsohon shugaban kasar murna game da kaddamar da littafin da ya rubuta kan yadda ya tafiyar da mulkin Najeriya.
Ranar Talata tsohon shugaban kasar ke kaddamar da littafin mai suna, My Transition Hours, don haka ne Shugaba Buhari ya yi kira ga ‘yan kasar su koyi da Mr Jonathan wajen rubuta irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban Najeriya.
Shugaba Buhari da tsohon shugaban kasar cif Olusegun Obasanjo na cikin mutanen da Mr Jonathan ya gayyata wurin kaddamar da littafin.
Goodluck Jonathan dai ya mika mulki a hannu Shugaba Buhari bayan ya kayar da shi a zaben shugaban kasa na 2015, abin da bai taba faruwa ba a tarihin kasar.
Amincewa da shan kayen da Mr Jonathan ya yi ya sa manyan kasashen duniya, ciki har da Amurka sun yaba masa.
Shi kansa Shugaba Buhari ya sha yaba wa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan kan arda da shan kayen da ya yi da kuma mika masa mulki ba tare da zubar da jini ba.
Sai dai Shugaba Buhari bai fasa caccakar tsoffin shugaban kasar ba, ciki har da Mr Jonathan, kan abin da ya kira “lalata kasar da kuma rashin aiwatar da ayyukan da suka dace duk da dumbun kudin da suka samu lokacin da suke kan mulki.”

Kotu Ta Hana Wa Jaafar Jaafar Cigaba Da Sakin Faya-Fayan Zargin Rashawa

LABARI DA ƊUMI-ƊUMI: KOTU TA HARAMTAWA JAAFAR JAAFAR CIGABA DA SAKIN FAYA-FAYAN ZARGIN KARƁAR RASHAWA NA GWAMNA GANDUJE.
Kamar yadda jaridar Solacebase ta ruwaito, ayau litinin 19 ga watan Nuwamba, Alƙalin Babbar kotun Kano Justice Namallam ya amince da buƙatar da Gwamna Ganduje na jihar Kano ya shigar gaban kotu na haramtawa Kamfanin DailyNigerian mallakin ɗan Jarida Jaafar Kaafar cigaba da sakin faya-fayan bidiyon dake hannunsa masu nuni da Gwamna Ganduje yana karɓar kuɗaɗe a hannun ƴan kwangila a matsayin Rashawa.
Baya da nan, kotun ta ɗage cigaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 6 ga watan disambar bana.

Hanyoyi 6 da za'a kare jiki da fata a lokacin hunturu (Sanyi)

Lokacin huturu lokacin ne da jiki da fatar mutane ke wahala matuka saboda kura da iskar da ake yawan fama da shi.
Kamar yadda aka sani hunturu kan fara a tsakanin watannin Nuwamba zuwa Maris ne. Wannan lokaci fatar mutane kan rika yakunewa yana karkarcewa wasu ma har budewa yake.
Matsalolin da irin wannan canjin yanayin ke kawowa sun hada da bashewar leben baki, tsagewar kafafen hanci, mura, da dai sauran su.
Ga hanyoyin.
1. A rika saka kaya masu nauyi kuma wadanda ke rufe jiki kaf da takalma da za su rufe kafafuwa domin kare mutum daga iska.
2. Za a iya shafa man kade domin shi man kade na da ingancin hana bushewar jiki.
3. A rika shan ruwa a kowani lokaci ba sai an jira an ji kishi ba.
4. Shafa mai a lebe da kafafen hanci domin kare su daga tsagewa.
5. A rika yin wanka da ruwan dumi musamman da safe ko kuma da yamma.
6. Za a iya cin abincin dake dauke da kitse, fiya, kifi domin suna dauke da sinadarin dake gyara fatar mutum.

Buhari ya nada surikin sa babban mukami

Shugaba Muhammadu Muhammadu Buhari ya amince da nadin wasu manyan mukamai biyar da kuma na wasu Manyan Daraktoci biyu na Hukumomin Gawamnatin Tarayya.
Cikin wadanda aka nada din har da surikin Buhari, mai suna Junaid Abdullahi, wanda aka bai wa shugabancin Babban Sakataren Hukumar Raya Yankunan Kan Iyakakokin Najeriya (BDCA).
An nada Junaid tun a ranar 22 Ga Satumba, kuma zai shafe shekaru hudu ya na shugabancin hukumar.
Ranar Juma’a ne Babban Sakataren Ayyukan Yau da Kullum na Ofishin Babban Sakataren Gwamnatin Tarayya, Olusegun Adekunle ne ya bayyana nade-naden na su a ranar Juma’a da ta gabata.
Kafin ranar Juma’a dai ba a sanar da cewa an nada surikin na Buhari a kan mukamin ba, an rufe batun, domin tun a ranar 22 Ga Satumba aka nada shi kan mukamin.

An baWa Ganduje ‘Amintaccen Gwamnan 2018’ duk da nuna shi kuru-kuru yana zira daloli na cin hanci a aljihun sa

Jaridar ‘The Telegraph’ ta nada Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje Gwarzon Gwamnoni na Shekarar 2018 duk kuma da zargin wawurar milyoyin daloli da aka nuno shi a cikin wani bidiyo ya na yi.
Jaridar ta ce ya samu lambar yabon ne a kokarin da ya yi a fanonin inganta shirin kiwon lafiya da kuma harkokin ilmi a jihar Kano.
Ganduje ya shiga tsomomuwa tun bayan da wata jarida mai suna ‘Daily Nigerian’ ta fallasa wasu bidiyo inda ya nuna shi ya na karbar damman daloli yana karkacewa ya zira su a aljihun jamfar sa.
Majalisar Dokokin Jihar ta kafa kwamitin bincike, inda har ta gayyaci babban editan jaridar, Ja’afar Ja’afar ya bayyana a gabanta.
Mako daya bayan an gayyaci Ja’afar, kwamitin ya kuma gayyaci gwamna Ganduje, amma ya noke, bai je ba, sai ya tura wakili.
Ana cikin haka kuma sai wani lauya mai suna Muhammad Zubair, daga kungiyar lauyoyi ta SDN, ya shigar da kara, ya nemi a dakatar da binciken da majalisar Kano ke wa Ganduje.
Kwamiti a karkashin shugabancin Baffa Dan’agundi ya ce zai ci gaba da bincike duk da karar da aka shigar.
Daga baya kuma mai shari’a A.T Badamasi na Babbar Kotun Kano ya sake bada umarnin a dakatar da bincike.
Bayan dakatar da binciken ke da wuya kuma, sai Ganduje ya maka Ja’afar Ja’afar da jaridar Daily Nigerian kara kotu, ya na neman a biya shi diyyar bata masa suna har ta naira bilyan uku.
Shi ma Shugaban Hukumar EFCC ya kira wani taron ‘yan jarida, ciki har da Jaafar Jaafar. A lokacin taron, an yi masa tambaya a kan me EFCC ke ciki game da zargin da aka yi wa Ganduje domin an nuno shi ya na karbar kudade?
Maimakon Magu ya amsa tambayar, sai ya ce a wuce wannan tambayar, a yi masa wata tambaya.
Ba za a iya gurfanar da Ganduje a kotu ba saboda ya na kan mulki, amma za a iya bincikar sa.
Kamar yadda aka binciki tsohon gwamna Ayo Fayose lokacin ya na kan mulki, sai da ya sauka sannan EFCC ta kama shi.
A wurin karrama Ganduje, Manajar Darakta na The Telegraph, Funke Egbemode, ta jinjina wa Ganduje sosai.
Funke har ila yau ita ce Shugabar Kungiyar Editocin Jaridu ta Najeriya, NGE.
Funke ta ce a cikin ‘kiftawar idanu’ Ganduje ya inganta harkokin ilmi da kiwon lafiya a jihar Kano.

Na kashe wa kamfen din Buhari makudan kudade a jihohi 30, amma bai saka min ba – Saraki

A cikin wani bidiyo da aka fallasa, Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya bayyana babban dalilin batawar sa da kuma haushin da ya ke ji wa Shugaba Muhammadu Buhari, cewa ya samo asali ne daga rashin gudanar da wasu ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ba ta yi ba jihar Kwara, duk kuwa da dimbin gudummawar makudan kudaden da ya bai wa tafiyar kamfen din Buhari a yakin neman zaben 2015.
Saraki kuma ya yi ikirarin cewa a lokacin yakin neman zaben Buhari a 2015, ya kashe kudi kusan naira bilyan daya a jihohi 30 daga cikin jihohi 36 na kasar nan, duk domin kamfen din Buhari.
Da ya ke jawabi a gaban wasu ‘yan jam’iyyar sa a jihar Kwara, Saraki ya ce gwamnatin tarayya ba ta da niyyar tsinana wa jihar Kwara da jama’ar ta komai. Ya ce da an bai wa ‘yan jihar mukamai kamar yadda aka fifita wasu bangarori, to da al’ummar jihar ba su shiga cikin kunci kamar yadda suke ciki a yanzu ba.
Maganganun da Saraki ya yi da harshen Yarbanci ya yi maganar ta tsawon minti 33, ga wasu magoya bayan PDP na jihar.
Tuni dai aka rika yada wannan kalami na sa a a soshiyal midiya.
Wani mai suna Kayode Ogundamisi ne ya fara watsa shi a shafin sa na twiter.
“Yayin da na bar PDP na koma APC, na sadaukar da kai na ina yi wa APC kamfen irin yadda ban ma taba yin kamfen a baya ba. Na yi rangadi jiha-jiha ina taya Buhari kamfen har lokacin da aka yi zaben 2015.
“Daga cikin jihohi 36 na kasar nan, na biya domin gudanar da harkokin zabe na jam’iyya har a cikin jihohi 30. Na raba naira milyan 400 a wasu jihohi, wasu milyan 300, wasu kuma naira milyan 200.
A jihohin Kudu maso Yamma ne kadai ban raba kudade ga kamfen din Buhari ba.
“Sai da ta kai ni har da baki na ke bai wa manajojin banki umarnin a fitar da kudade . Tunanin mu a lokacin idan an yi nasara za a aka wa mutane na da manyan mukamai, kamar yadda aka rika saka wa wasu mutanen wani yankin.
“Ku kan ku na sha fada muku a lokacin kamfen cewa idan ranar rantsuwa ta zo, tare ma za mu tafi Abuja, domin ina sa ran za a ba ku manyan mukamai irin su hukumomin FERMA, NITDA, NPA ko UBEC da sauran su.”
Saraki ya yi korafin yadda a karon farko a kasar nan, bayan zaben 2015, Shugaban Majalisar Dattawa da Kakakin Majalisar Tarayya ba su iya sawa a dauki ko da mai shara aiki ko su dauka da kan su.
Yayin da jama’a da dama ke bayyana damuwar su a kan bidiyon, da dama na cewa Saraki ya fadi abin da ke cikin zukatan jama’ar kasar nan da dama, musamman daruruwan wadanda suka taimaka wa Buhari da makudan kudade, amma ya watsar da su ko ya yi musu butulci.
Sai kuma ofishin Saraki ya maida martani a kan muryar da aka ce ta Saraki din ce.
Kakakin Yada Labarai ya ce masu adawa ne ke neman ko ta yaya sai sun kauda Saraki, kuma hakar su ba za ta cimma ruwa ba. Ya ce duk abin kirkira ce, ba gaskiya ba ne.

Yadda Aka Samu Nasarar Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Zamfara

DA DUMIDUMINSA
An Yi Nasarar Kama Masu Garkuwa Da Mutane A Zamfara
Daga Dauda Umar Januhu
Labarin da muke samu shine da sanyin safiyar yau ne ‘yan kungiyar sakai suka yi nasarar kama uku daga cikin masu garkuwa da mutane a wata bata kashi da suka yi da barayin a garin Kadamutsa dake karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara.
Allah ya kara tona masu asiri.

Tsantsar Gaskiya Da Rikon Amanar Atiku Ne Yasa Na Aure Shi -Titi Abubakar

Tsantsar gaskiya da rikon amanar Atiku ne yasa na aure shi -Titi Abubakar
Hajiya Titi Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP Alh Atiku Abubakar ta bayyana dalilan da yasa ta yi sha’awar auren mijin nata tun fil-azal.
Hajiya Titi Abubakar ta ce tsantsar gaskiya da rikon amana da kuma gaskiyar mijin na ta ne yasa ta aure shi.
Titi ta bayyana hakan ne a lokacin da ta karbi bakuncin wata kungiyar mata magoya bayan mijin na ta da suka kai mata ziyara a gidan ta dake a garin Abuja.
Matar ta Atiku ta kuma kara da cewa a kullum idan ta ji ana cewa mijin ta bai da gaskiya da rikon amana,lamarin na bakan ta mata rai sosai saboda ta san karya ce tsagwaron ta da kuma yarfe na siyasa.

Ba Lallai Bane Sule Lamido Ya Marawa Atiku Baya A Zaben 2019

Ba lallai bane Sule Lamido ya marawa Atiku baya a zaben 2019 – Umar Danjani
Akwai alamun cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, na iya janye goyon bayan da yake yiwa dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben kujerar shuganan kasa.
Mr. Lamido, na daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar kujerar shugaban kasa a PDP, sai dai sun sha kasa a zaben fitar da gwani da ya gudana makonnin da suka shude.
Da yawa daga cikin yan takarar, shun sha alwashin marawa Atiku baya don tunkude shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari daga kujerarsa a zaben 2019.
Sai dai, Umar Danjani, mai tallafawa Mr. Lamido na musamman, ya ce ubangidansa bai ji dadin yadda kwamitin gudanar da yakin zaben jam’iyyar PDP ya mayar da shi saniyar ware ba, tun bayan kammala zaben fitar da gwanin.
A ranar Alhamis, a wani taro na masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da ya gudana a sakatariyar jam’iyyar na jihar da ke garin Dutse, Mr. Lamido ya yabawa wakilan jam’iyyar kan zaben, inda ya bayyana cewa zaben da suka yi ne har ya baiwa wasu yan takara samun nasara.
“Dukkanin wanda kuka zaba, walau a matakin jihar ko kasa, shine yau yake da nasara, kuma kunyi ne don kashin kanku, sai dai gaskiya guda daya, shi son kai kullum ke kai mutum gada-na-sani,”a cewar sa.
Wata majiya da ke da kusanci da Mr Lamido, ta shaidawa jaridar Premium Times cewa, Mr Atiku bai yiwa Mr Lamido adalci ba, kasancewar Lamido na daya daga cikin wadanda suka reni jam’iyyar PDP, kuma baitaba canja akala ba, sai dai an mayar da Lamido saniyar ware a harkokin jam’iyyar tun bayan da Atiku ya samu nasara a zaben fidda gwani.
Majiyar ta ce:”Abun da mamaki matuka, yadda suka gudanar da taro a Dubai da Abuja amma babu wanda aka gayyaci Lamido ko aka yi masa bayani kan abubuwan da suka faru.
To wata kila dai ko taron na iyalan wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar ne don naga shugaban majalisar dattijai da kuma Kwankwaso a taron.”
“Haka zalika, Mr Danjani,ya shaidawa Premium Times cewa, kwamitin yakin zaben dan takarar shuga

Buhari Zai Kaddamar Da Kamfen A Abuja:2019:

2019: Buhari zai kaddamar da kamfen aAbuja
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da kamfen din takarar shugabancin Najeriya a karo na biyu yau a dakin taro dake fadar shugaban kasa.
Idan ba a manta ba hukumar zabe ta dage dokar hana gudanar da kamfen ne daga Asabar 18 ga watan Nuwamba.
A karon gaddamar da kamfen din tazarce na shugaba Buhari ana sa ran gaggan ya’yan jam’iyyar APC duk za su halarci wannan taro.
Ministan makamashi da Ayyuka, Tunde Fashola ne zai bude fili da yin bayanai kan ayyukan da gwamnati ta ke yi tun bayan darewa karagar mulki a 2015.
Sannan kuma ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ya dora daga inda Fashola zai tsaya.
Ministan Kudi za ta yi bayani kan irin kokarin da gwamnatin Buhari ta yi duk da karancin kudaden shiga da take samu tun daga 2015 zuwa 2018.
Minstan Ayyukan Gona, Audu Ogbe da Maryam Uwais duk zasu bayani kan ci gaban da aka samu zuwa yanzu a kasar nan.
Bayan haka za a nuna bidiyo har guda hudu domin nuna irin ayyukan da gwamnati ta yi kuru-kuru ba a takarda ba kawai domin kowa ya shaida ba hira bace ko boge, yadda aka fadi haka aka yi.
Shi Babban abokin hamayyar sa, Atiku Abubakar zai Kaddamar da na sa Kamfen din a gobe Litinin amma a shafin sa na Facebook.

Hackers Sun Barnata Wa Mutani Sama Da Miliyan Ashirin Account

Hackers Sun yiwa Sama Da Mutane Miliyan 50 Kutse A Facebook
A watan da ya gabata kamfanin Facebook ya tabbatar da cewa akwai adadin masu amfani da shafin sama da Miliyan 50 wadanda masu kutse (Hackers) sukayi nasarar shiga account dinsu.
Ma’ana dai wasu sunyi kutse sun samu bayananka na facebook wato posting dinka da private chat dinka, hotuna da videos d.s ba tare da izninka ba.
Facebook sun tabbatar da cewa suna iyakar kokarinsu wajen ganin sun bada kariya ga bayanan abokanan hurdarsu.
A satin da yagabata an gabatar da babban taro na majalisar wakilai ta yanar gizo ta duniya wato “Internet Governance Forum” a birnin Paris na samu bibiyar taron daga nan gida Nigeria bisa jagorancin cibiyar #CITAD wadda ta tsara yadda za’a yi taron damu daga nan gida Nigeria.
Acikin darusan da aka tattauna akwai “Cybersecurity da Cyber Harm” wanda suke da jibi da bayanan mutum akan internet da sauran na’urori na zamani, to ina so na ja hankalin al’umma kadan da su sani cewa.
Duk wani abu da kayi a social media to wannan kamfanin social media din suna da copy din duk bayananka.
Haka duk wani application da ka saka a wayarka ka lura da kyau akwai doka da ka’idar su kuma mafi yawa akwai sharadin zasu dinga ganin bayananka.
Akwai masu diban hotuna wasu lambobin wayarka wasu sauti wasu videos don haka ayi kokari a kula don gudun zaije yazo, koda babu hackers yakamata mutum ya san akwai wannan.
Dangane da hackers kuma munsha yin bayani a baya akan yadda ake kare kai daga fadawa tarkonsu

`Yan Shi`a Sun Ja Kunnen Kakakin Rundanar `Yan Sandan Jihar Kano, SP Musa Majiya

‘Yan Shi’a Sun Nemi A Ja Kunnen Kakakin Rundanar ‘Yan Sandan Jihar Kano, SP Musa Majiya
Daga Bilya Hamza Dass
A wata takardar manema labarai da mabiya Shi’a suka fitar dauke da sanya hannun Ibrahim Musa Shugaban dandalin yada labarai na mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya a ranar 18/01/2018, sun bayyana cewa suna neman rundanar ‘yan sanda taja kunnen kakakinta akan kalaman kyama da ya keyi akansu.
Hakan yabiyo bayan sanarwan da kakakin yabar yan kan cewa an kama wani tsohon dan Shi’a yana hada baki da wani korarren dan sanda wajan karban kudin Jama’arsa bisa zalunci wanda yace suna cigaba da fadada bincike kan hakan, wanda tuni ‘yan Shi’an suka musanta zargin.
Takardar ta kara da cewa “Wannan ba shi ne karon farko da SP Majiya ke amfani da duk wata ‘yar damar da ya samu ba wajen bakanta Shi’a. Don haka muke kira ga rundunar ‘yan sanda ta tsawata masa, tare da tuna masa cewa ya guji amfani da matsayinsa wajen cimma wata manufa ta akidarsa.
Muna kuma kira ga jama’a da su yi watsi da maganganun da SP Majiya ya yi na nuna cewa Shi’a tana maraba da masu aikata miyagun laifuffuka. Sanannen abu ne cewa ‘yan Shi’a musulmin kwarai ne da suke gudun duk wani nau’in aikata muggan laifuka” Inji shi Ibrahim Musa.

Zamfara Ta Dawo Gidan Jiya: An Yi Garkuwa Da Mutum 45 A Shinkafi




Bayanai na nuna cewa, an sace mutum 45, ciki har da mata da kananan yara a karamar hukumar Shinkafi, wannna sace sacen sun faru ne a tsakanin ranar Alhamis zuwa ranar Asabar. Lamari na farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a kan hanyar garin Kware zuwa garin Shinkafi inda aka yi awon gaba da mota dake dauke da mutum 35 a kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a garin na Shinkafi, inda aka kwashe dukkansu zuwa cikin daji na nufin yin garkuwa da su.

 Bayanan da suka fito daga wani day a bukaci a sakaya sunansa, ya nuna cewa, dukan muytane 35 sun fada hannun masu garkuwar ne a lokacin da suke kokarin fito da motarsu bayan da ra makale a cikin yashi. Daga nan ne suka ga ‘yan ta’addan sun fito su da yawa a kan mashina dauke da muggan makamai, inda suka zagaye mutane suka kuma yi awon gaba da su.

 An kuma ruwaito cewa, haka kuma a ranar Asabar, a yi sace mutum 11 ciki har da mace daya a kuyen Kware duk dai a cikin karamar hukumar Shinkafi, bayanai sun kuma nuna cewa an kashe mutum daya a lokacin da aka kawo harin. Jamiin watsa labarai na rundunar ‘yan sanda na jihar SP Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwa lamarin, ya ce, tuni a kan tura wata kakkarfar runduna ‘yan sanda don shawo kan wanna lamarin a karamar hukumar Shinkafi. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu dukkan bangarorin jami’an tsaron jihar ciki har da sojoji sun shirya gudanar da ayyukan fatattakar ‘yan ta’adda daga dukan maboyarsu. 

SP Mohammed ya kuma kara da cewa, ‘yan sanda za su yi dukkan abin day a kamata na ganin an cafke ‘yan ta’addan gaba daya tare da kuma hukunta su.