Zaben cike gurbi: Ahmed Babba-Kauta ya doke dan uwan sa wajen lashe zaben dan majalisar dattawa

Ahmed Babba-kaita ta doke dan uwansa wajen lashe zaben dan majalisar dattawa

Ahmed Babba-Kaita ya doke yayar sa Kabir Babba-kaita a zaben da aka gudanar ranar asabar 11 ga watan Agusta.

Dan takarar jam'iyar APC Ahmed Babba-Kaita ya doke yayan sa mai wakiltar PDP a zaben cike gurbin kujerar dan majalisar dattawa na arewacin jihar Katsina da aka gudanar ranar asabar.

Hukumar zabe ta sanar da sakamakon zaben ne inda tace dan takarar APC ya samu kuri'u 224,607 yayin da dan takarar PDP ya samu 59,724.

Ahmed Babba-Kaita ya doke yayar sa Kabir Babba-kaita a zaben da aka gudanar ranar asabar 11 ga watan Agusta.

Hukumar zabe tace an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata matsala ba.

Yan gida sun fafata ne domin cike gurbin tsohon dan majalisar dattawa Sanata Mustapha Bukar wanda ya rasu cikin watan Afrilu na bana.

Sakamakon zaben Katsina shine wanda aka tabbatar da wanda yayi nasara cikin zaben cike gurbi hudu da ukumar ta gudanar.

An gudanar da zaben ne a jihohin Katsina, Bauchi, Kogi da Cross-rivers. A jihohin Katsina da Bauchi an gudanar da zaben dan majalisar dattawa yayin da aka gudanar da zaben dan majalisar wakilai na tarraya da na jiha a jihohin Kogi da Cross-rivers.

Sai dai zaben Kogi ta tada kura inda rahotanni ke nuna cewa an samu matsalar satar akwatuna wanda ya sanadin rasa rayuka.

No comments:

Post a Comment