Dalilin Daya Sa Nafi Yiwa Mata Waka – Ado Gwanja



Ga tattaunawar da jaridar Aminiya tayi dashi

Aminiya: Mene ne tarihin rayuwarka a takaice?

Gwanja: An haife ni a Unguwar Birged da ke birnin Kano. Sai dai asalin mahaifina dan garin Warawa ne, yayin da mahaifiyata Shuwa Arab ce daga garin Maiduguri a Jihar Borno.
Na yi karatun firamare a Makarantar Babbangiji da ke Karkasara. Sannan na yi sakandare a Sakandiren kofar Nasarawa. Bayan na gama ban ci gaba da karatu ba sai na rika zuwa kasuwa wurin mahaifina.
Bayan mahifina ya rasu ne sai na shiga buga-bugar rayuwa har Allah Ya kawo ni matsayin da nake a yanzu.

Aminiya: Mutane da dama sun san Gwanja a fina-finan Hausa sai kuma ga shi ka canja sheka zuwa waka, yaya aka yi hakan ta kasance?

Gwanja: To a gaskiya dama waka na fara, domin na fi shekara 12 ina yin waka, sai dai a wancan lokaci ba a san ni ba. A wancan lokaci nakan rubuta waka tun ba ni da kudin zuwa situdiyo na buga har na rika zuwa ina bugawa. Ko ta yi dadi ko ba ta yi ba ban damu ba, ni dai na san ina waka. To bayan wani lokaci kuma sai na shiga harkar fim.

Aminiya: Yawancin lokuta an fi ganin kana fitowa a matsayin dan Daudu a fina-finan Hausa, haka ka fi mika akalar wakokinka a kan mata, me ya jawo haka?

Gwanja: To batun fina-finai da nake yi a dan Daudu wannan yanayin labari ne ya zo da haka, kasancewar na yi abin da ake bukata a wasu fina-finai da aka ba ni wannan matsayi to sai ya zama cewar in dai labari ya zo da hakan sai a nemo ni a ba ni. Amma ba ni nake zabe ba.
Shi kuma batun waka da ake ganin na fi yi wa mata, zan iya cewa saboda su ne iyayen biki. Bahushe ya ce inda baki ya karkata ta nan yawu kan zuba. Kowa ya san irin rawar da mata ke takawa idan aka zo harkar biki, kin ga kuwa tunda ina yin wakokin biki, to dole da su za a yi.

Aminiya: Baya ga wakokin fina-finai da kake yi da na biki kana yin wakikin siyasa?

Gwanja: Eh ina yin wakoki ga ’yan siaysa, idan dan siyasar da kansa ya nemi hakan. Abin da ba na yi shi ne ba na yin waka in kai wa dan siyasa, saboda na san halinsu sai a hankali.

Aminiya: Yaya dangantakarka da sauran mawaka?

Gwanja: Gaskiya akwai alaka mai kyau a tsakaninmu, don akwai girmamamawa a tsakninmu. Ba ma yi wa juna hassada ko bakin ciki.
Aminiya: Wane ne gwaninka a fagen wakoki?

Gwanja: Ba ni da gwanin da ya wuce Aminu Maidawayya.

Aminiya: Kasancewar an fi daukarka don yin wasa a bukukuwan aure, mutane na zargin cewa ba ka zuwa biki ko amsa gayyatar talakawa, mece ce gaskiyar wannan batu?

Gwanja: Gaskiya abin ba haka yake ba. Ai abin ba kudi ba ne, domin wani ma za ka iya yi masa kyauta ya danganta da yanayin mu’amalarku.Ina ganin duk mutumin da ya zo ku yi mu’amala ya mutunta ka, domin a da bai zo wurinka ba.
Haka kuma wata rana ba zai zo wurin naka ba. Kawai ni abin da na sani shi ne ba a fin karfin masoyi. Masu yin wadannan kalaman suna yi ne don ba a yi musu kyauta-kyauta ba ko kuma ma kai-tsaye in ce kyauta. Kowace sana’a sunanta sana’a dole mutum ya yi hakuri ya bi yaddda tsarin abu yake wajen.

Aminiya: Wane tallafi mawaka ke samu daga gwamnati?

Gwanja: Ni zan iya cewa tsawon rayuwarta a wannan fage ban taba jin labarin gwamnati ta ba mu tallafi ko wani abu makamancin haka ba. Idan ka ga gwamnati ta waiwaye mu, to so take ta yi amfani da mu don cimma wata bukatarta ko kuma idan ana neaman mu biya haraji.
Gwamnati ba ta kallonmu a matsayin wadanda suka rage mata nauyin neman aiki, domin akalla ban da nauyin kanmu da muke dauka muna da yara da ke aiki a karkashinmu wadanda ta nan suke samun abin da suke kula da iyalansu.

No comments:

Post a Comment