
Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ta tura sojin kundumbala da jiragen yaki jihar Kaduna da ke arewacin kasar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Ibikunle Daramola, ya aike wa manema labarai ranar Litinin da safe ta ce an tura sojin kumdumbala ranar Lahadin da ta gabata domin tallafa wa jami’an tsaron-ciki da ke aiki a jihar.“Sojin kumdumbalar za su hadu da sojin saman da ke Kaduna da sauran jami’an tsaro domin su tabbatar an daina kashe-kashen rashin hankali da ke faruwa a wasu sassan jihar,” in ji sanarwar.
Ta kara da cewa tun ranar 22 ga watan Oktoba aka tura da jirage masu saukar-ungulu biyu da jirgin yaki samfurin DA-42 Intelligence Surveillance and Reconnaissance (ISR), wadanda suka rika shawagi a wuraen da ake rikici.
Rikici ya barke a birnin Kaduna da wasu sassan jihar, musamman garin Kasuwan Magani, mako biyu da suka wuce.
Lamarin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Kazalika gwamnatin jihar ta sanya dokar hana zirga-zirga da zummar dakile rikicin, ko da yake an sassauta ta a birnin Kaduna da kewaye.
Ko da a ranar Juma’a sai da wasu matasa a garin Gonin Gora da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja suka toshe hanya da zummar far ma matafiya.
Sai dai jami’an tsaro sun tarwatsa su.
Matasan garin sun sha tare matafiya suna kashe su da zarar an soma rikici a birnin Kaduna.
Daga bisani Gwamna Elrufai ya halarci wurin domin ganin matafiya basu fuskanci wata matsala ba.
Ranar Asabar, gwamman ya ce zai tashi garin na Gonin Gora dungurungun idan matasan garin suka ci gaba da tare mutane suna kashe su.
Da yake jawabi a filin “Hannu a Yawa” na gidan rediyon tarayya na Kaduna, Gwamna Elrufai ya ce “ina ba mutanen Gonin Gora shawara cewa wannan abin da matasansu suke yi su daina idan ba haka ba wallahi tallahi zan tashi garin.”
“Ba za mu yarda su rika rufe hanya su hana mutane shiga ko fita daga gari suna kashe su ba. Za mu sa jami’an tsaro su rika duba wurin amma idan ba su daina ba, garin da kan shi bai fi karfin gwamnati ba.”
Gwamnan na Kaduna ya yi wannan jawabi ne daidai lokacin da gwamnatin jihar ta ce ‘yan sanda sun cafke mutum 32 wadanda ake zargi da hannu a rikicin jihar.
No comments:
Post a Comment