SHA'AWA DA ABABAI DAKE KARIN SHA'AWA DA KUMA YADDA ZA'A MAGANCE MATSALAR AL'AURA


Yan uwana mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin Iyayen Giji…
Kamar yadda ku ka sani shi wannan shiri a na yin shi ne, don matan aure zalla, domin ba su shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su Inganta Rayuwarsu, kamar gyara zaman takewarsu da mazajensu da mu’amalarsu ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki, irin abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci domin inganta lafiyar jikinmu da samun dauwamammiyar ni’ima da kuzari a jikkunanmu.
To, uwar gida ba sai na yi miki dogon bayani ba, wannan makon ma shirin zai dora daga inda ya tsaya. Saboda yawan tambayar da na ke samu daga ’yan uwa mata yawancinsu su na Ć™orafin ba su san meye sha’awa ba ko su ce ba su da sha”awa sam, siyasa na yi tunanin fadada bincike na a kan sha’awa. Don haka ku biyo ni:-
Mece Ce Sha’awa?
Sha’awa dai wata aba ce da Allah Ya halitta kuma ya sanya ta tsakanin halittun mutane da dabbobi bakidayansu. Allah ya na sanya sha’awa cikin zukata, don samun natsuwa da annashuwa da kuma zaman lafiya a tsakanin masoya. Ita sha’awa ta na da rai kuma ta na mutuwa, idan ba ta samun kulawa yadda ya kamata.
Bambamncin Sha’awa Tsakanin Mace Da Namiji
Kowane daga cikinsu Allah ya saka ma sa sha’awa gwargwadon tasa. An halicci mace da sha’awa 99 shi kuma namiji ya na da guda daya.
A likitance kuma an tabbatar akwai wani sinadari, wanda gwargwadon yawansa a jikinki gwargwadon yawan sha’awarki, kuma a na kiran wannan sinadari da ‘testosterone’ da turance. Amma bincike ya tabbatar cewa na maza ya fi yawa, sai dai na mata ya fi kaifi, amma ya na iya dakushewa kamar yadda wuka ta ke dakushewa. Mafi yawan mata wannan sinadarin a dakushe nasu ya ke, domin sha’awarsu ba ta karfi.
Dabarun Gigita Da Dimaucewa
A cikin karshen farjin mace akwai wata tsoka a tsakiya. Ita wannan tsoka Allah ya yi ta babu macen da azzakari zai taba wannan gurin face sai ta samu kanta cikin gigita da dimauta har ta kasa mallakar kanta. Amma kuma wannan gurin ya na iya samun matsala in har ya dakushe a dalilin wasu abubuwa kamar “sanyi ko basir”. Macen da ta ke jin salam babu gamsasshen dadi lokacin da a ke tare da ita, to ya na iya zamowa ko ciwon sanyi ko basir ne su ka kama ta.

Cututtukan Da Su Ke Damun Al’aurar Mata
Kamar yadda bincike ya nuna cewa, akwai cututtuka da yawa masu damun al’aurar ‘ya’ya mata, kama daga balagarsu zuwa fara daukar ciki har zuwa daina al’adarsu, kamar:-=====
(1) Warin gaba (odour): Warin gaba na ‘ya’ya mata ya na samuwa saboda wasu dalilai da su ke jawo shi kamar haka:
1- Tafiya ba wando.
2- Kin wanke farji bayan jima’i.
3- Kin wanke farji da ruwan zafi; misali bayan an yi al’ada.
4- Barin wando ya kai kwana uku a jiki.
5- Kama ruwa da ruwa mai sanyi karara.
6- Kin wanke gaba bayan an tsuguna a masai.
7- Mace ta ringa biya wa kanta bukata da hannu ko wani abu.
Ki sani cewa wari ya na fitowa daga gurare uku; hammata, farji da baki. Saboda haka lallai ne ki bada kulawa ta musamman a wannan guraren naki, don gudun samun matsala.
(2) Kumburin Gaba (Inflammatory) da kaikayin gaba (wato Emetic): Wannan cututtuka su ma su na damun al’aurar ‘ya’ya mata kwarai da gaske.
(3) Zafin Gaba (Pain).
(4) Zubar Ruwa (Leaking).
(5) Rashin Haihuwa (Infertility).
(6) Sanyi Ko Zafin Mahaifa:
Wadannan su ma su na hana mace ta samu ciki saboda illolin da su ke tattare da hakan.
Karin Bayani:=============
Akwai cututtuka da yawa da su ke samun al’aurar mata, saboda ba ta rabuwa da danshi wanda ta nan ne wasu kwayoyin halitta su ke samun zama a cikin al’aurar tasu. A na kiran su Micro–organism da Turanci.
Kusan cewa shi farji da a ke magana a kan cututtukansa shi ne wanda Allah Ya halitta da wani sinadari na mayen karfe da wata tsoka kuma ta na da baki guda biyu hagu da dama. Yayin da sha’awar mace ta motsa sai ta rika motsi dai-dai kuma ta na iya yin rauni har ta daina motsi. Wannan tsoka kamar fulogi ne a jikin mace. Yayin da ta yi ma ta yawa, sai ta kasa motsi. Daga nan sai sha’awar ‘ya mace ta dauke, domin ita wannan tsoka ita ce ke feso wani ruwa wanda shi ke sauko da wani ruwa da ya ke da jin dadin mu’amalar jima’i kuma ya ke sa wani zaki tsakanin mace da miji. Idan daya daga ma’aurata ya sami matsala, sai ka ga auren ya ki zaman lafiya. Amma idan babu matsala sai ka ga a na zaune lafiya cikin shauki da annashuwa.
Mafi yawa mata masu ciki su na kamuwa da cututtuka daga wasu kwayoyin halitta da ke rike al’aurar mata, saboda gabansu ba ya rabuwa da danshi. Wadannan kwayoyin halittu su ne, bacteria, fungi da sauransu.
Alamomin masu nuni izuwa kamuwar cutar al’aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawo shi. Kadan daga ciki:-
Zafi yayin fitsari. (burning during urinate) .
Ciwo daga wajen a’aurarta (Itching out side the bagina) .
Canzawar gaba ba kamar yadda ta saba gani ba.
Zafi yayin saduwa da miji (discomfort during sedual intercourse) .
Abubuwan Da Su Ke Kara Shaawa
Yawaitar cin kayan itatuwa su na karawa sinadarin da ke samar ko tayar da sha’awa karfi, Tasly Phytoestrogen.
1) Kankana: za a samu kankana a hada ta da gwanda a feraye a markada su a ‘blender’ a sha. Za a samu ni’ima a jiki.
2) Dabino: za a samu danyen dabino wanda ya fara nuna a dinga ci. Shi ma ya na kara ni’ima.
3) Zogale: cin kwadon zogale a yanka mi shi kwai ya na kara ni’ima kuma ki samu zogalenki mai kyau ki shanya shi a inuwa. Idan ya bushe, sai ki daka shi ki rika sha da madara. Ya na kara ni ‘ima sosai.
4) Ya’yan Zogale: uwargida ta samu ’ya’yan zogale ta bar su su bushe ta dake su a hade da dabino da cikude ta dinga sha da nono. Za ta yi mamaki sosai.
5) Lemon Aya: aya da kwakwa uwargida za ki samu ayarki ki jika ta ta jiku sosai sai ki yanka kwakwarki kanana ko ki gurza a greader ta ki haka kwakwar da ayar ki markada ki tace ki sa sugar ko zuma ki sha. Za ki sha mamak.
6) Ganyen Idon Zakara: ki samu ganyen idon zakaran ki hada shi da dabino ki daka shi, ki dinga sha da nono.
7) ZAITUN: macen da ta ke fama da bushewar farji za ta samu zaitun ta sha cokali biyu, sannan ta dinga zubawa a farjinta. Insha Allahu za a dace.
8) Kwakwamba: ’yar uwata za ta samu cocomber ki feraye ta yanka tumatir da albasaki yanka dafaffen kwai guda uku, sai ki ci. Shi ma ya na kara ni’ima sosai.
9) Ruwan Rake: za ta samu ta kirba rake a turmi ta samu abin tata mai kyau ki matse ruwan, ki saka zuma cokali biyu. Za ki samu ni’ima sosai kuma ki ringa shan rake da yawa.
10) AYA: haka kuma ’yar uwata za ki samu aya ki wanke ta ki nika ki soya sama-sama ki cire jan bawon. Za ki samu cukwi da dabino ki hada su gabadaya ki daka ki dinga sha da nono ko madara.

No comments:

Post a Comment