Yadda Zaku Kasance Koda Yaushe Acikin Koshin Lafiya Da Cikakken Jini _ Ganyen Ugu



Ganyen Ugwu wani babban labari ne ya kuma fi kabewa, bugu da kari kuma wani maganin jini ne wanda ya fi blood tonic, yanzu masu ilmin kimiyya sun gano amfani da kuma muhimmancin kabewa wajen rage radadin zafin ciwon sanyin kashi wato sickle cell wajen jarirai da kuma manya. A wani sabon nazarin da aka yi ‘yan Nijeriya masu bincike cewar kabewa na rage yiyuwar kamuwa da cutar sanyin kashi, a tsakanin jarirai da kuma manyan mutane. Tana yin hakan ne wajen hana da kuma samar da daidaituwar red blood cells ko kuma jajayen jini, wadanda sun kunshi cutar Sikila, wadanda su aikinsu shi ne su kai jini duk inda ya dace a jikin mutum, ya mayar dasu yadda suke da, ya kuma rage yawan nau’in sickle wanda yake cikin haemoglobin da kuma ‘red blood cell’. Masu bincike sun yi bincike da kuma nazarin wani nau’in sinadarin etanol da kuma wani abhu daga kabewa, (Telfairia occidsentalis) suka kuma sata cikin jinin da aka samo daga, marasa lafiya wadanda suke fama da cutar sanyin kashi an kuma tabbatar da hakan. Suna kuma tsakanin shekaru 12 da kuma 30 suna kuma cikin koshin lafiyarsu, bayan haka kuma suna zuwa wani dan karamin asibitin haematology wanda ke karkashin asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo dake Ile- Ife. Rahoton binciken na shekarar 2018 wanda aka wallafa a mujallar magungunan gargajiya da kuma na zamani, suynn hada da Mojisola C.Cyril- Olutayo da Joseph M.Agbedahunsi da kuma Norah O.Akinola dukkaninsu daga jami’ar Obafemi Awolowo ta Ile-Ife jihar Osun. An lura da muhimmancin dake akwai na yakar cutar sanyin kashi da kuma da sinadarin Ciklabit sai kuma nutraceutical wajen maganin cutar sanyin kashi da kuma ta rashin isasshen jini da Cajanus cajan (pigeon pea) a matsayin wani babban al’amari sai kuma phenylalanine wanda shi ma yana da muhimmanci.
Da farko dais u masu binciken sun yi ani aiki a jihohin Ondo da kuma Osun dangane dasu magungunan gargajiyar, wanda kuma ake amfani dasu a gargajiyance, wajen maganin cutar sanyin kashi da kuma ta rashin isasshen jini. An dai samu kabewa saboda yadda ake ta yawan magani da ita wajen kamar irin wanda ke kara jini, da kuma maganin cutar sanyin kashi. Ana kiran da suna kabewa Telfairia occidentalis wanda ake kira da suna Ugwu da harshen Ibo Aworoko Eweroko cikin harshen Yoruba, Ikong ko kuma Umce a harshen Ibiobio da kuma Umuke a harshen Edo. Kabewa wadda aka yi mata kayan tanadi tana da dadi sosai wadda ake amfani da ita a sassa daban daban na Nijeriya, ana dafa ta a matsayin miya, ko kuma amurza ta cikin ruwa ko kuma cikin giya a ba adanda basu lafiya, wadanda suke da matsalar rashin yawan jini, saboda hakan yana kara yawan jini a Kudu maso yammacin Nijeriya. Bugu da kari kuma ana yinn amfani da kabewa wajen maganin cutar sikari, hakanan ma amfani da ganyen wanda ake amfani da shi a matsayin magfanin karin jini, wajen maganin zazzabin malaria da kuma maganin rashin jin dandanon wani abu. Ganyen Kabewa ya kunshi sinadaran K, Cu, Iron da kuma Mn sai kuma muhimman amino acid da kuma hanyar samun karin wasu sinadaran magnesium da kuma zinc, sanin kowa ne suna muhimmanci ga mutane da kuma dabbobi. Masu binciken sun gano cewar ganyen kabewa wanda sarrafa an samu 4mg/ml hakan kuma ya samar da babban amfani wajen yaki da cutar sanyin kashi, fiye da Ciklabit, akwai kuma namijin aiki a daidai yaan mizanin da aka sa shi. Idan kuma aka yi la’akari da yadda shi ganyen kabewa yake bada maganin ciwon sanyin kashi, idan akja sa shi kadan ko kuma akla sha shi kadan, sun bayyana cewar ana iya amfani da bani bangare nata a matsayin prpphylatic wajen maganin matsalolin da cutar sanyin kashi ke haifarwa, ko kuma ayi amfani da shi wajen rage radadin zafin ciwo. Kamar dai yadda su masu binciken sinadaran amino acids da tron da bitamin C, an gane cewar lallai suna da raarc da zasu taka wajen maganin matsalolin cutar sanyin kashi, wadannan kuma gaba daya, suna taka muhimmiyar rawa wajen damar da take da ita wajen karya lagojn cutar sanyin kashi. Bayan haka kuma ita kabewa ta kunshi babban sinadarin dake yaki da ita cutar sanyin kashi da kuma yadda ita kabewa yadda take taka rawa akan red blood cells.
Matsalar red blood cells kom kuma jajayen jini abin ya na dan raguwa dai dai lokacin da su kwayoyin halittar suke karuwa, duk wani maganin daya yawan su red bloode cells, ta yadda ake kara rashin karsashinsu, sai suka fahimci cewar ashe da shi ganyen kabewa da aka sarrafa yana dakushe duk wani karsashin sickle red blood cells ya kuma hana matsalar5 da zata shafi kwayar halitta, wanda kuma hakan na iya shafar babban aikin red cell wajen yin aikin shin a kai jini dukkanin wuraren da suka dace. Kamar dai yadda suka bayyana wajenn yin magani da amfani da su ganyayen, wadnda suke amfanin yadda su ganyayen suke hana, da kuma maida komai kamar yadda yake danganeb da halin da red bloodcells ya shiga, ga kuma maganar ragowar matsalar da su sinadaran suka shiga babban abinda yafi dacewab ke nan. Ganyayen da ake maganinn gargajiya dasu a nahiyar Afirka musamman ma a Nijeriya, wajen yin maganin sanyin kashi wanda maganinsu bbab kasafai wasu suka sani ba a gargajiyance. A gargajiyance da ake yi dawasu ganyaye sunn hada da maganin rage yaduwar ciwo a jiki, karin jini, da kuma maganin shiga wata matsala. Amfani da hydrodyurea shi ya daukaka samun saukin cutar sanyinn kashi, amma shi ma wannan wani lokaci akan samu tashi matsalar. Wadannan magungunan wadanda ganyaye ne wadanda suka hada da Zanthodyllum danthodyloides, Canjanus (pigeon pea) pawpaw Cnidoscolus aconitifolius (efo Iyana Iyana ko kuma spinach da dai sauransu. Ku san yara 150,000 ake haihuwarsu da cutar sanyin kashi duk shekara a Nijeriya,, kuma kashi 50 na wadannan yaran ne suke mutuwa kafin sukai shekaru goma, idan kuma aka kiyasta kusan kashi bakwai na yara a yawan al’ummar dniya suke dauke da kwayar..........,

No comments:

Post a Comment