Matsaloli Da Maganin Karin Ni'imah Ke Wa Mata


Mata da yawa a wannan zamani sun fi fifita amfani da magungunan mata na karin ni’ima fiye da komai a rayuwar aure wanda hakan ba daidai ba ne.
 Ya na da kyau mu san wasu abubuwa da ke da muhimmanci cikin dukkanin rayuwar aurenmu ba mu rike bangare guda mu ce shi ne kawai zai yi mana jagora ba.
Mu koma can baya a rayuwar iyaye da kakanninmu, mu duba yadda su ka yi rayuwar su shin ya yi iri daya da yadda muke yin namu a yanzu? Amsar ita ce a’a, saboda mun saka son zuciya da kiwa da gaggawa a cikin zamantakewar mu. Iyayen mu sun yi zama cikin aminci da mazajensu da ganin girman juna da daraja juna, rayuwar aurensu ta yi karko ta kuma zama abin kwatance. Yanzu me ya sa ba za mu yi koyi da su ba?
Mu sa ni a irin wannan wuri mu da kanmu mu ke samarwa kan mu matsala mai girma. Ban ce kar ayi amfani da wadannan magunguna ba amma dai ya na da kyau mu yi amfani da abin da ke da inganci son samu ya zama na ainahi ta yadda mu ka san a wurin wacce mu ka saya tare da tabbacin ingancinsa da kuma ta san abin ko ya san abin sosai. Dalilin fadin haka shi ne a yanzu mafi aksari ma su sayar da wadannan magunguna sun yi yawa ta yadda har sai in an bincika sosai ake samun ma su inganci don masu sayar da na bogi su su ka fi yawa a harkar.
Wadanne matsalolin wadannan magunguna na mata ke Haifarwa?
Wadannan magunguna na haifar da matsaloli ma su tarin yawa kadan daga cikin su sun hada da :=======
1:Ya na haifar da cuta a cikin mahaifa.
2:Yana jawo matsala a gaban mace na samun cutar da za ta ki warkewa ko ta ki jin magani.
3:Ya na haifar da cutar daji a gaban mace.
4:Ya na jefa mace ta rasa kudi a hannunta saboda duk in da ta ji ana sayar wa sai ta kai kudinta can.
5: Ya na haifar da rashin nutsuwar zuciya.
6. Ya na jawo mutuwar aure.
Da sauransu.
Ina Mafita?
Mafita anan su ne :
1:Ya na da kyau mata mu tsaya a wuri daya.
2: Mu nemi abubuwan da ke kewaye da mu na ainahi (natural) mu rike, sun fi amfani ga jiki da lafiyar mu.
3. Kar ya zama komai mu ka gani ba tare da bincike ba mu doru a kai.
4:Mu zama masu samar da wasu hanyoyin samun irin wadannan kaya masu inganci.
5:kar ya zamanto rayuwar auren mu dukka mu dora ta a kan amfani da magungunan mata.
6:Bayan wannan mu zama masu ladabi, taka tsan-tsan, hangen nesa, iya girki, ado da kwalliya hakuri don rayuwar aurenmu ta zama da inganci kamar ta iyaye da kakannin mu.
Shawara
Mata mu zama masu kula da sanin muhimmanci lafiyar mu, wadannan magunguna akwai wadanda ke da illa ga rayuwar mu, mu sani Allah da Ya halicce mu ya hallice mu da ni’imar mu wanda wani lokaci yawan amfani da wadannan kayan mata kan kashe wasu abubuwa a jikinmu wadanda ke da matukar muhimmanci, mu zama masu yawan alaka da rake, mangoro, kankana, madara, dabino, romon kaza, da abinci ma su kyau da gina jiki sauran mu barwa Allah don shi Ya san daidai

No comments:

Post a Comment