Takaitaccen Tarihin ALi Nuhu


An haifi Ali Nuhu Muhammad a 15 ga watan march shekara ta 1974, shi jarumi ne na bangarori daban-daban hada daga Nollywood, Kannywood, da kuma ketare a takaice dai Ali Nuhu jarumi ne na Africa gaba daya. Bayan kasancewar sa jarumi sannan mashiryin film ne, marubuci, kuma mai daukar nauyi. Ana masa lakabi da Sarkin Kannywood saboda jajircewar sa da kuma kamun kai.
An haifi Ali a garin Borno, Maiduguri ta arewacin Nigeria. Sunan mahaifin sa Nuhu poloma dan garin Balanga Gombe mahaifiyar sa Fatima Karderam Digema yar Bama ce a garin Borno. Ya girma a Jos da Kano. Ya karanta Geography a jami'ar Jos sannan yayi bautar kasa a garin Ibadan, Oyo. Ba a nan Ali Nuhu ya tsaya ba ya cigaba da neman ilimi musamman ta fannin sana'ar sa wata film inda yaje jami'ar California domin daukar darasi akan hada fina-finai. Ali Nuhu ya fara shirin Hausa a shekara ta 1999 inda ya fara a matsayin jarumi, ya fito a fina-finai 260 na Hausa sannan 150 na turanchi. Ali Nuhu shine jarumin da yafi kowane jarumi karbar lambar girmamawa mai ma'ana a Kannywood inda ya fara da karbar gwarzon jarumi a shekara ta 2005, Gwarzon matashi a 3rd Africa movie academy award, Gwarzon shekara  a the future award, Gwarzon shekara a Zulu African film Academy award 2011 da sauran goma sha hudu da ya karba a wurare daban daban.
Yana da mata daya mai suna Maimuna Ali Nuhu da yara biyu. Ali Nuhu ya kasance fuska ta Kannywood.
Wannan shine takaitaccen tarihin Ali Nuhu Muhammad daga shafin DAULAR MASOYA

No comments:

Post a Comment