Abubuwan Dake Karawa Hakora Haske
Lura da
hakori na daya daga cikin hanyoyin dakan kara fitar da kima hadida
kamalar mutum. Duk yadda mutum yakai ga iya kwalliya hadida kwarewa
wurin daukar wanka daxarar yagaxa tafannin kula da hakoransa saikaga
gabadaya kwalliyar ta lalace, dankuwa yagaxa tafannin bawa hakoransa
kulawar data dace. Danhaka wannan wata hanyace daxata dawowa mutum kima,
martaba hadida darajar hakoranki/ka koda kuwa hakoran sunyi irin baki
ko tsatsa tacikine haka kuma yakan yaki kwayoyin cutar dakan haifarwa
mutum warin baki.
1-STRAWBERRIES:Kinemi ganyen
itacen strawberry kiyankashi kanana- kanana kidinga cuda hakoran dashi,
yana sanya hakora haske sosai haka kuma yana kore dattin dake makalewa
ajikin hakora, hakanan yana sanya baki fitar da iska me dadin kamshi.
2-LEMON
ZAKI(Orange): Kisamu lemon xaki mekyau meruwa kiyanka kimatse ruwan
sannan ki guntsi ruwan abakinki sannan kisanya brush kidinga diddirxawa
lungu da sako sannan kixubar kiwanke da ruwa. Yanasa hakora suyi kashar
kamar kankara. 3-LEMON TSAMI(LEMON) Kisamu lemon tsami kiyanka ki matse
ruwan sannan ki sanya abakinki kiwanke kowane lumgu da saki na bakin,
yana fitar da duk wani dabbara- dabbara dakan makale a hakori.
SIRRIN FARAREN HAKORA
Yawancin
mutane ba su da masaniyar yadda zasu magance matsalar rashin fararen
hakora wasu har suna zaton halitta ne, to ga hanya mai sauki Kamar
yadda kowane sashi na jikin dan Adam yake bukatar kulawa, haka zalika
Hakora ma na bukatar kulawar mai su. hanyoyin da za’a bi cikin sauki
don samun lafiyayyun hakora masu haske da sheiki har ma su rika walkiya.
Hanyoyi sune kamar haka:
Dabi’ar cin abinci
Da farko dai sun bayyana cewa dole mutum ya canja dabi’arsa ta cin
abinci, ma’ana mutum ya kasance yana cin abubuwa mai gina jiki, kuma
yana da kyau ya gujewa cin abincin da yake da tarin sukari a cikinsa
(Sugar). Ta’ammali da abubuwan da suka da hada Madara, Nono da kuma shan
wadaccen ruwa mai tsafta da sauransu yana inganta lafiyar Hakori
Amfani
da Danko (Chewing Gum): Taunar Danko wato wanda aka fi sani da Chewing
gum a turance yana taimakawa matuka gaya wajen hana zaman wani abu a
cikin sakon hakori, a sanadaiyyar hakan ka iya jawo tsutsar hakori dama
sauran dangogin matsalolin da suka shafi hakorin baki daya. Amfani tare
da
sauya magogin baki (Toothbrush): Yana da
matukar muhimmanci, wanke baki akai-akai domin yin hakan zai taimaka
wajen wanke tare da fitar da duk wani nau’in abun da ya makale a
hakorin. Haka zalika yana da kyau ace mutum yana sauya magogin bakinsa
duk tsawon wani lokaci (a kalla duk bayan wata uku). Bayan amfani da
magogin baki yana da kyau ace an wanke da ruwa mai tsafta sannan a barsa
ya bushe tare da samar masa wajen ajiya mai kyau, amma kar ya zama ana
barinsa a bayan gida (Toilet) kamar yadda wasu suka maida dabi’arsu,
wanda hakan ka iya jawo wasu kwayoyin cututtuka su hau kan shi magogin
bakin. Hanyoyi 8 da za ku bi domin Association, ta bayyana cewa kaso
42% ne na mutane ke amfani da magogin baki domin kula da lafiyar hakori.
Sun sake jero wasu hanyoyin da suke ganin yin su zai taimaka gaya wajen
samuwar ingantattun hakora; Wanke baki da magogi har na tsawon mintuna
biyu (2 Minutes) akalla sau biyu a rana. Kuskure baki da ruwa lokaci
zuwa lokaci, musamman bayan kamala cin abinci ko wani abu mai dauke da
abun da zai iya zama a hakori. Amfani da maganin wanke baki wanda da
dama daga cikinsu suna dauke da sinadarin kariya (Antibacterial) wanda
yana taimakawa wajen wanke duk wani abu tare da karawa hakora kwari.
Ganin
Likitan Hakori: ziyara ga likitan Hakori yana da matukar amfani, saboda
yin hakan zai taimaka wajen duba da irin halin da hakoran ke ciki,
sannan in har akwai wani abu da yake damun hakoran, likitan zai iya bada
shawara ko magani domin kauda cutar tun kafin ta zama babba. Likitan
zai iya yin wankin Hakori wanda hakan zai bawa mai su damar jin dadi
sosai, kuma yana da kyau ake yin wanki hakori akalla sau daya a
shekara.
Karin amfani da sinadarin Vitamin:
Kamar yadda bayanai suka gabata cewa, a kaucewa cin abubuwa masu sukari
da yawa, a nan kuma an bayyana cewa amfani da abinda yake dauke da
sinadarin Vitamin zai taimaka sosai. Cin abinci mai dauke da ganyayyaki
kamar su kabeji, Salak, lansir,Zogale da sauran Ganye yana da amfani.
Cin kayan itatuwa kamar lemo, Ayaba, Kankana, Inibi duk suna da fa’ida
sosai wajen lafiyar hakori. Har wayau, cin abinda ya shafi nau’in abinda
ke cikin ruwa kamar su Kifi, da sauransu wanda duk suna dauke da nau’in
Vitamin D zasu taimaka gaya.
Amfani da Man
Kwakwa: Mutum zai iya amfani man kwakwa wajen wanke baki. Cokali daya
na man kwakwa mutum zai diba ya wanke bakinsa har na tsawon mintuna 20
har sai yawun bakin mutum da man kwakwar sun canja launi zuwa launin
madara, sannan a zubar amma fa kar a hadiye.
Mutum
zai iya hada man wanke baki da kansa Makilin (toothpaste) i Akwai
abubuwa da akan yi amfani da su domin hada abun wanke baki, wannan
abubuwa su ne kamar haka:
Cokali 4 na hodar Calcium
Cokali 1 na Stevia Cokali 1 na Gishiri (salt)
Cokali 2 na Baking Soda
Kaso ¼ na kofin man kwakwa
Wadannan su ne jerin hanyoyin da in kunyi amfani da su zasu taimaka wajen kara tsaftar hakori tare da kara musu inganci.
Allah ya saka da alkairi
ReplyDelete