Maganin 15 da Baure Keyi



Tsawon shekaru aru-aru, 'baure wani nau'i ne na dangin kayan marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya.
Wani sabon bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka da dama kama daga ciwon suga zuwa cututtukan fata.
 'Baure ya kunshi sunadarai da dama masu gina jiki da suka hadar da fiber, antioxidants, vitamin A, vitamin C, vitamin K, B vitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron.
 Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2016 ya tabbatar da cewa, sunadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon suga.


Ga wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam:======

1. Magance kwarnafi da tashin zuciya.

2. Hawan jini.

3. Bunkasa lafiyar zuciya da jini.

4. Ciwon daji wato cutar Kansa.

5. Rage nauyin jiki.

6. Inganta lafiyar mazakuta da kuma ni'imar ma'aurata.

7. Magance ciwon basir mai tsuro.

8. Cutar farfadiya.

9. Tace mafitsara.

10. Tasiri wajen inganta lafiyar fata.

11. Zazzabi.

12. Ciwon Kunne.

13. Cututtukan fata (Karzuwa, makero, maruru, kirci, kyazbi).

14. Bunkasa lafiyar hanta.

15. Cutar asma da dangin cututtukan da suka shafi hunhu.

No comments:

Post a Comment