
Ga jerin sunayen yan wasan Nijeriya da suka sauya kungiya a bayan kammala kasuwar siyar da yan wasa a nahiyar turai.
Yayin da kasuwar siya da siyarwar yan wasan kwallo ya kai karshe, ga wasu fiatattun yan wasan tawagar super eagles ta nijeriya da suka sauya kungiya gabanin fara kakar bana.
Cikin jerin yan wasan akwai wadanda suka koma sabon kungiya bisa matakin aro. Hakazalika akwai wadanda suka sauya kungiya domin nuna bajinta a wata nahiya da sabon kungiya.
Ga sunayen su da sabon kungiyar da suka koma kamar haka:
Ahmed Musa
Dan wasa mai tauraro zai nuna kwarewar sa a kasar Saudiya tare da tawagar kungiyar Al-nassr. Ya koma kungiyar daga Leicester na Ingila.
Leon Balogun
Mai tsaron bayan tawagar Nijeriya ya koma kungiyar Brghton & hove na Ingila daga Mainz dake Jamus.
Moses Simon
Hazikin dan wasan gaba ya bude sabon babi a rayuwar sa na dan kwalo inda ya koma taka leda da tawagar Levante dake karawa a gasar La liga na kasar Andalus. Ya koma kungiyar ne daga kungiyar KAA Gent.
Alhassan Ibrahim
Tsohon dan wasan Kano Pillars da Akwa United ya koma kasar Portugal da murza leda. Dan asalin jihar Kano wanda aka fi sani da Muazam ya koma kungiyar Clube Desportivo Nacional.
Oghenekaro Etebo
Zazzafar dan wasan tsakiya ya koma Stoke City na Ingila daga Fc Feirense na kasar Portugal.
Tyrone Ebuehi
Shima dan wasa wanda ya nuna bajinta wasan Nijeriya da Iceland a gasar kofin duniya na bana ya koma kasar Portugal. Ya koma shahararren kungiyar nan ta Benfica. Ya koma Kungiyar daga ADO Den Haag na kasar Holland.
Henry Onyekuru
Matashin dan wasan gaba ya koma kasar Turkiya da murza leda da tawagar kungiyar Galatasaray. Dan wasan wanda bai samu damar nuna gwanitansa a gasar kofin duniya sakamakon raunin da ya samu ya koma Galatasaray kan matakin aro daga kungiyar Everton dake Ingila.
Bryan Idowu
Hazakakurin dan wasan bayan super eagles ya koma Lokomotiv Moscow dake fafata a gasar kasar Rasha.
Muhammed Shehu
Tsohon jagoran tawagar matasan yan wasan Nijeriya shima ya sauya sheka daga Istanbul Baseksehir zuwa HNK gorica dake kasar Croatia.
Sadiq Umar
Fitaccen dan wasa mai hengen raga abokan adawa ya koma Rangers dake kasar Scotland bisa matakin aro daga kungiyar Roma na kasar Italiya.
No comments:
Post a Comment