Hadiza Bala Ta Sa Jami`anta Kallon `Juyin Sarauta` –Gidan Dabino

awancin kwararru a masana’antar shirin fim ta Kannywood sun yi ittifakin cewa, Fim din Juyin Sarauta ya sha bamban da irin finafinan da a ke shiryawa a masana’antar ta Kannywood ta fuskar kashe kudi, nuna tsantsar al’adar Bahaushe da kuma tsaruwa.
Fitacciyar marubuciyar nan, Hajiya Balaraba Ramat ce ta dauki nauyin shirya shi, yayin da fitaccen marubuci kuma jarumi, MALAM ADO AHMAD GIDAN DABINO, ya ke jagorantar shirin.
A kwanakin baya a jiyo duriyar fim a babbar sinimar da ke babban birnin tarayyar Najeriya a na nuna wa jami’an hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Najeriya.
Editan LEADRSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, ya samu zantawa da Gidan Dabino kan wannan batu da ma wasu da dama. Ga yadda tattaunawar ta kasance a tsakaninsu: A kwanakin baya an gudanar da wani taron kallon fim din Juyin Sarauta a Abuja.
Shin yaya yanayin taron ya ke kuma su wa a ka nunawa fim din? Taron nuna fim ɗin da a ka yi a Abuja, an yi shi ne musamman don manyan jami’an tashohin jiragen ruwa na Afrika ta yamma. Wato su ne suka zo gidan sinima na Silberbird mu ka nuna mu su.
Me ya sa a ka zabi a nunawa wadannan jami’ai?
An zabi a nunawa manyan jami’an tashohin jiragen ruwa na yammacin Afrika ne saboda Babbar Daraktar Hukumar Jiragen Ruwa ta Nijeriya Hadiza Bala Usman ce mu ka gayyata wajen taron gabatar da fin ɗin da muka yi a Kano, amma ba ta sami damar zuwa ba sai ta nemi mu zo mu nuna ma ta tare da ma’aikatanta, shi ne kuma abin ya zo daidai da taron da su ke yi na yammacin Afrika shi ne aka haɗa  aka jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya.
To, mu na iya cewa ba su da alaƙa, amma su mahalarta taron ai mutane ne masu jini a jiki kuma wasu daga cikinsu suna son kallon fim wanda ya shafi al’ada da kuma masarautu, saboda haka kuma sun bar ƙasarsu zuwa wata ƙasa suna buƙatar shaƙatawa da kuma ganin wasu abubuwa waɗanda ƙila ba daidai suke da na ƙasarsu ba, wannan wani ilmi ne daga cikin ilmai da ake samu a tafiya. Ka ga a nan su a kan knsu sun sami wani ilmi wanda ƙila in suna can ƙasarsu ba za su sani ba. A nan aikin su ya jawo sun ilmantu da waɗannan abubuwa da suka gani.
Wacce fa’ida za ku samu ko su su samu a wannan kallon fim din? Fa’idar da mu mu ka samu ita ce, mun tallata Juyin Sarauta ga wasu muta da ba ƙasarmu ɗaya ba, sun gani sun yaba sun kuma tofa albarkacin bakinsu a hirarrakin da muka yi da su bayan kammala kallon fim ɗin.
Sun kuma tafi da hoton labarin Juyin Sarauta a zuciyoyinsu. Su kuma sun amfana da kuma ji daɗin kallon fim ɗin kamar yadda suka faɗi da bakinsu a cikin faifan bidiyon da muka yi hira da su. Mun yi musayar adireshin juna ko da wata rana mun je ƙasashensu za mu iya haɗuwa da juna mu yi hulɗar arziki, tun dama ita t haɗa mu a Abuja.
Fa’ida kuma ta gaba ita ce hukumar Jiragen Ruwa ta Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Hajiya Hadiza Bala Usman ta ba mu abin goro na wannan ɗawainiyar nuna fim da muka yi a silimar Silberbird, Abuja.
Tun da silimar mu muka haye ta, mu muka sayi ruwa da lemo da guggurun da kowane mai kallo ya ci ya sha a lokacin kallon. Kuma fim ɗin Juyin Sarauta ne fim na farko cikin harshen Hausa daga Kannywood da aka taɓa nuna a wannan silima.
Me ku ka fahimta daga gare su bayan kammala kallon fim din kuma me su ka ce a kansa?
Mun yi hira da wasu baƙin daga ƙasashen yammacin Afrika sannan ita ma mai gayya mai aiki Hajiya Hadiza Bala Usman mun yi hira da ita, duk sun ji daɗi sun yi farin ciki d ganin wannan fim sun yaba sosai da sosai, kai har a gidan Rediyon Muryar Amurka Sashen Hausa, Nasiru Adamu Elhikaya ya sanƴa hirarrakin.
Yaushe za a kai Juyin Sarauta sinima, don mutane da yawa su samu damar zuwa su kalli dalilin da ya sa ya ke ta samun cinye kyautukan gasa?
Fim ɗin Juyin Sarauta za a fara nun shi a silimar Ado Bayero Mall da ke kan titin gidan Zoo a Kano, ranar 2/11/2018 kuma za a yi kwana 14 ana nunawa, duk masu son kallonsa suna iya zuwa can daga ranar 2 zuwa 16 ga watan Nuwamba, tun daga ƙarfe 10 safe har zuwa 10 na dare kullum za a nuna sau hudu.
Me ya sa har yanzu bai fito kasuwa ba?
Abin d ya sa fim ɗin Juyin Sarauta bai fita kasuwa ba har yanzu, saboda kasuwar CD ta ja baya, a irin wannan yanayi babban kuskure ne ka saki fim mai tsada  kasuwa ba tare da ka bi wasu hanyoyi na dawo da wasu kuɗaɗen ba, don haka yanzu hanyoyin muke dan bi kafin kuma nan gaba mu sake shi a kasuwa.
Me za ka kara wanda ba a tambaye ka ba? Abinda zan ce shi ne, fim ɗin juyin Sarauta ya sha bamban da sauran finafinai da ake yi a Kannywood, don gidan sarkin da aka yi amfani da shi gina shi muka yi, wasu kayan ɗinkasu muka yi wasu mauka sayo a kasuwa wasu muka hayo.
Kuma labari ne da aka gina shi n tarihin masarauta a ƙasar hausa kimanin shekaru ɗari da suka wuce. B mota b keke, b babur, ba wutar lantarki ba rediyo. Don hak aiko ne babba wanda ya lashe kuɗi sama da Naira Miliyan Ashirin da takwas, N28,000,000.
Don haka ya kamata masu son kallon fim n alada su garzayo silimar Ado Bayero da ke Kano kalle shi. Manyn kmfanoni kuma su yi hoɓɓasa su ga sun bayar da tallukansu a cikin wannan fim.

No comments:

Post a Comment