Shugaba Buhari Bai Bamu kudi ba - Inji Rabiu Rikadawa

Fitaccen jarumin fim din Hausa, Rabi’u Rikadawa wanda aka fi sani da Dila ya bayyana cewa duk wanda ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba su kudi a lokacin da suka kai masa ziyara ba gaskiya ya fada ba.
“Duk wanda ya fada maka an ba ‘yan fim da suka je wajen Shugaba Buhari kudi to ba gaskiya ya fada ba, kowane ne shi.”

Rabi’u Rikadawa ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya zo yin aikin wasan kwaikwayo na BBC media action a Sakkwato a makon da ya gabata, inda ya ce ziyarar da suka kai ba wanda aka tursasa sai ya je, “Maganar akwai bambancin ra’ayi masana’antarmu ai ko dan da ka haifa a cikinka sai ka same su da bambancin ra’ayi. Haka ne a duniya gaba daya, amma ita tafiya in za ka yi ta za ka nemi masu irin ra’ayinka ka yi tafiya da su don haka muka je ba don a raba mana kudi ba.

“Duk mutumin da hankali ya ratsa shi yakan dubi rayuwa ce ya ge me gaba za ta samar don samun rayuwa mai inganci. Mun dubi tsarin shugaba Buhari mai yin aiki ne da mutane za su amfana, ba wai ya dauko kudi ya baka ba.

“Dubi yadda ya daudo aikin wuta na Mambila, ga aikin hakar mai a Bauchi da Borno da Katsina. Irin wadannan abubuwa da kishinsa ga Arewa muka ga ya kamata mu goyi bayansa.

“A ziyarar mun samu nasara ya fahimce mu ya san halin da muke ciki a masana’antarmu, na abun da ya fi ci mana tuwo a kwarya ta satar fasaha da ake mana. Misali a nan Sakkwato kana iya samun mutum miliyan 7 a cikinsu za a samu miliyan 2 da ke kallon fim din Hausa, amma za ka samu dubu 100 da ke sayen fim dinmu wajen masu satar fasaha suke saye. In an hana satar fasahar nan muka rika samun ko rabin masu kallonmu suna sayen fim gare mu, kudin da muke kashewa za su rika dawowa. Kuma mun yi godiya da tallafin bashi da gwamnati ta baiwa wasunmu suna jujjuyawa.”

A game da kallon da mutane ke musu a matsayin masu bata al’ada da tarbiyar Bahaushe, cewa ya yi, “Ba ka isa ka kawar da mutane daga tunaninsu ba sai dai yau da gobe a hankali domin wannan al’ummar tana da wuyar daukar sauyi. Ko masallacin fadar Sarkin Kano da aka sanya lasifika sai da aka yi zanga-zangar cewar an kawo bidi’a sai da aka turza kafin aka karbi canjin. Duniya gaba daya canjawa take yi, in ka ki canjawa sai ka zama bigidaje.
“Da ganin wasu fim ka san an shigo da malaman, har lambar yabo sun ba wasu daga cikinmu. Lamarin ba dole kowa ya gamsu da kai ba, in ka ci karo da abin da kake so ka dauka.”

No comments:

Post a Comment