Yadda Akayi Jana’izar Janar Idris Alkali A Abuja

An yi jana’izar Janar Idris Alkali mai ritaya a Abuja, babban birnin Najeriya ranar Asabar da rana.
Mutane da dama ne – ciki har da babban hafsan sojin kasa na Najeriya Janar Yusuf Buratai – suka halarci jana’izar Janar din, wanda aka kashe a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar kasar a watan Satumba.
A ranar Laraba ne rundunar sojojin Najeriya ta gano gawar Janar din a wata rijiya da ke Gushwet a gundumar Shen ta karamar hukumar Jos South a jihar Filato.
Kwamandan runduna ta uku ta dakarun kasar, Birgediya Janar Umar Mohammed ya ce daya daga cikin wadanda suka mika kansu ga ‘yan sanda ne ya nuna wa sojoji rijiyar, wadda “ba a amfani da ita.”

Yadda aka gano gawar

“Kamar yadda aka sani, mun sanar da bacewar Manjo Janar Idris Alkali ranar 3 ga watan Satumba.”
Ya kara da cewa “Saboda haka ne muka bazama nemansa, kuma mun gano motarsa wadda a cikinta muka gano wasu daga cikin kayansa, kuma wannan ne ya bayyana mana cewa wani mummunan abu ya same shi.”
“A makon jiya kuma mun gano wani kabarin da aka tone, wanda ya ta tabbatar mana da cewa an kai gawarsa wani wuri bayan an fara binne ta a wurin.”
Hukumomin sojin kasar sun yi shelar neman wasu mutum 13 da suke da hujjar cewa suna da hannu wajen bacewar marigayin.
Mutanen sun hada da hakimin gundumar Du, Yakubu Rap da Pam Gyang Dung wanda direban motar bas ne da Timothy Chuan da kuma wasu masu aikin gyaran bodin mota Da Chuwang Samuel wanda aka fi sani da Morinho da Nyam Samuel wanda shi kuma aka fi sani da Soft Touch.
“Wasu daga cikin wadanda ake neman sun kai kansu ga ‘yan sanda, a cikinsu ne wasu suka nuna mana wannan rijiyar, inda muka gano gawarsa”, inji Janar Mohammed.
Kawo yanzu, rundunar sojojin Najeriya sun ce sun kammala bangarori biyu cikin uku da aka umarce su su yi.
Na farko shi ne an gano gawar marigayin. Na biyu kuma shi ne an gano motarsa, wato samfurin Toyota Corolla.
Janar Mohammed ya bayyana mataki na uku da ya rage a dauka.
“Abin da ya rage shi ne hukunta duk wadanda ke da hannu a wajen aikata wannan mummunan laifin, kuma duk wanda aka samu yana da hannu, komai girmansa sai ya fuskanci hukunci.”

No comments:

Post a Comment