Muhimmancin Wanke Hannu A Kowani Lokaci

Ma’aikatan kiwon lafiya sun bayyana cewa wanke hannu da ruwa da sabulu na kare mutum daga kamuwa daga mugan cututtuka.
Ma’aikatan sun bayyana haka ne a taron ranar wanke hannu na shekara-shekara da aka yi a Abuja.
Taron a bana mai taken ‘ Tsaftattacen hannaye mabudin samun ingantaciyyar kiwon lafiya” zai kara wayar wa mutane kai game da mahimmancin wanke hannu.
Kamfanin ‘Detol’ a nata tsokacin ta yi kira ga iyaye da malaman makarantu kan koya wa yara dabi’ar wanke hannu da sabulu da ruwa domin karesu daga kamuwa da cututtukan kan yi sanadiyyar rayukan su.
Taron ya kuma bayyana haka:
1. Koya wa yara dabi’ar wanke hannuwa da ruwa da sabulu na kare su daga kamuwa da mugan cututtuka.
2. Mafi yawan mutanen Najeriya basu wanke hannayen su da ruwa da sabulu.
3. Ya zama dole a rika wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.
4. Wanke hannu da ruwa da sabulu na rage yawan mace-macen mutane.
5. Ya zama dole wa ma’aikatan kiwon lafiya su rika wanke hannayen su da ruwa da sabulu kafin da bayan sun duba marasa lafiya

No comments:

Post a Comment