Anya! Ciwon Ya Mace Na Mace Ne???
Cikin kasala na zauna zuciyata cike da bacin rai da takaici, yayin da can cikin zuciyata sake sake suka yi min yawa tamkar zuciyata zata fashe. Wata sassanyar ajiyar zuciya na sauke, lokaci guda kuma na dubi Salwa dake zaune a gefen inda nake zaune, tana ta danna waya cikin nishadi nace mata, “Tsakani da Allah wannan wacce irin rayuwa ce Salwa?, a ce mace sam bata kishin ‘yar uwar ta mace, Amma in wajen karin magana ne, yanzu zaka ji an ce wai ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne, wanda karya ne sam ba haka ba ne “,.Nayi shiru daidai nan Salwa ta kece da dariyar mugunta tare da duba na tace, “wai duk rashin zabar Hajiya Madinar ne a matsayin ‘yar majalisa ya dame ki?, Nikuwa ban yi mamaki ba sam, don tabbas na san hakan ne zai faru, duk kuwa da yawan matan nan masu zabe, wanda da kuri’ar su kadai zamu iya kayar da Alhaji Madani wanwar, amma abin mamaki wai matan ne da kan su suka yaki ‘yar uwar su mace da kan su”,tayi shiru tare da duba na don ganin yaya maganar ta ta ke tasiri a kwakwalwata, sannan ta cigaba da cewa, “Sam ni ban yi mamakin ganin hakan ba, na ma san za’ayi hakan tabbas, Mata ne fa, kishin macen nasu a iyakar lebe yake, sam bai kai zuci ba, don Mace ce da kan ta ke yakar mace ‘yar uwar ta wurjanjan cikin kowanne hali”,.Na bi ta da kallon amincewa a lokacin da na fara nazarce nazarcen wasu halaye na mata iri iri.
Ginshiki
Kalmar nan ta ciwon ‘ya mace na mace ne ya gama duniyar kwakwalwar kowacce mace da ke ban kasa, ciki kuwa har da mata masu karancin shekaru, sai dai kash, abin takaicin shine mata na amfani da kalmar ne iya lebe, ba wait don ta tasirantu a kwakwalwar su ba, Domin yadda mace ke cin dunduniyar mace abin zai ba da mamaki ainun in aka yi la’akari da kalmar ciwon ‘ya mace na mace ne. Akwai wurare da dama da mata ke cutar da mata ‘yan uwan su sosai, Misali…..,
Aure:
Za a ga mace na yaki hauka hauka wajen hana mijin ta auren wata, wanda zata dauki abin tamkar yaki.In kuwa har aka taki sa’a macen ta shigo gidan, to shikenan an shiga sabuwar gaba da fitina wadda zata rayu muddin rai, yara da jikoki, kai har ma tattaba kunne .
Takara
A wannen bangaren kuwa in mace ta fito takara, to tabbas mata ne zasu hada kai su yi duk iyakar yin su don ganin sun kayar da ‘yar uwar ta su mace, sun zabi namiji akan ita ‘yar uwar su mace.
Asibiti
Idan kuwa a ka zo fagen asibiti mata mu na ji mu na gani, idan za mu asibiti zamu dinga adduar Allah ya sa mu samu namiji maimakon mace, saboda shine zai tsaya ya saurare mu, ya ji abinda ke damun mu, sabanin mace da za ta dinga hantara da nuna kosawa da gajiya, in ba’ayi sa’a ba ma fada da cin zarafi ya biyo baya, ga uwa uba rashin tsayawa ta ji takamaimai me ke damun ka.
Makaranta
Shi ma hakan ne dai a wannan bangaren, ko a makaranta ne malama mace kan zama mai tsauri da matsi ga ‘yan uwanta mata ainum, wani lokacin ma kiri-kiri mace za ta sa ‘yar uwarta mace faduwa a jarraba, ba wai don macen ta gaza ba, a’a!, kawai sai don keta da mugunta.
Ma’aikata
A nan ma a na yin ta domin ana samun tata burza kwarai, domin in mace ta zama babba a ma’aikata, to fa masu jin dadin ma’aikatar sai maza, matan da ke aiki karkashin ta kuwa to tasu ta same su kenan wajen matsi da takura.
Kasuwanci
A nan kuwa sai dai mu ce to fa. Domin kiri kiri mace na kasuwanci, amma ‘yan uwanta mata ba za su iya siye wajenta ba, don kar su kara mata arziki ta samu kudi, a maimakon haka gara su tsallake su taimaki kasuwancin namiji, maimakon na mace ‘yar uwarsu, ba don komai ba, sai don kyashi.
A nan abinda ya dace a duba shi ne shin me ya sa mata ke haka? Ina su ka ajiye kalmar ciwon ‘ya macen tasu? Ire-iren wannan halaye na mata kan mutukar daure min kai, har na fara tunanin shin zamani zai zo da mata zasu zubar da wannan tunani nasu da halayya su kama ‘yan uwan su mata, su hada kai, su tabbata tsintsiya madaurin ki daya?. Lallai wannan mafarki ne dana ke fata da mafarkin tabbatar sa, ba kuma da dadewa ba.
Domin wannan halayyar da ke tasiri tsakanin mu ne ya janyo maza har su ka samu hanya da damar kara tarwatsa mu, kawunanmu na kara rarrabuwa a koyaushe.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment