Kusakuren da Mata Ke yi Gurin Zama Da Miji



Akwai mata a suna, akwai kuma wadanda suka cancanta a kira da sunan, duk wata mace tsayayyiya ta san cewa duk wani dan’adam, malami ne ko almajiri, mai kudi ne ko talaka yana da abin yabo, kuma bai isa ya tsira daga wasu abubuwan da za a koka a kai ba, maigidanta ma haka, mutum kowani lokaci tara yake, ba wani wanda yake da sifar kamala ta ko ina in ba Allah SWT ba, haka duk inda mutum ya kai da kuskure dole kuma yana da wasu dabi’u wadanda za a yaba masa, don haka kada kuskuren namiji su sa mace ta dena ganin halayensa na kirki da kyawawan dabi’unsa, mace mai karamin tunani ita ce za ta dauki aibobin mijinta ta sanya su a gaba ta yi ta lugwigwita su kamar shan mangwaron kauye.
Ba bankaura mace kamar wacce ke bayyana duk wani kuskure da mijinta zai yi sai kowa ya sani, a karshe in ya zo da tsautsayi sai ta kwana a ciki, sai ki ji mace na cewa “Ni wallah ban damu ba ya auri kowa ma amma banda wance, ai wannan cin amana ne” amma fa na ga macen da ta kawo wa maigidanta wata kawarta ta ce ya aura, kuma wallahi ya aura din, duk suna zaman lafiya suna kaunar juna, kenan matsalar ba a auren kawa ba ne, sakin baki ne a yi ta hirar maigida da wadanda bai dace a ce sun ji ba, daga baya a ce “Sai da ta gama sanin sirrina sannan ta ce za ta aura min miji? Wallahi ba ta isa ba”.
Matsalolin maigida ba yadda za a ce ba za a magance su ba, ki yi duk abin da za ki iya wajen ganin kin warware matsalolinki, amma kar ki rika yawo da sirrorin gidanki, wani sa’in duk abubuwan da kike ganin ba su yi miki ba wata wannan abin ne ya yi mata, shekarun baya muka sami labarin wata da take ta kukan cewa maigidanta ya yi mata yawa, kullum sai ta yi zancen da kawarta, ashe ita kawar tana fama da karanci, dole ta rabu da maigidanta ta zo kuma ta aure mata miji, sai ranar auren aka yi ta tonon silili, wadanda da ba su san komai ba duk suka ji sirrorinsu, a banza kuma uwargidan ta fita ta bar wa amaryar gidan, ba wanda ya taba jin sirrinsu, komai zan-zan kenan, na ce da haka ake maganin mai shegen surutu.

Wasu matan suna da fahimtar cewa ba sa samun cikakkiyar kulawar mazansu in ba suna rashin lafiya ba, don haka komai kasawar cuta sai su langwabe su karairaye su fitar da rakinsu a fili don su farauci kulawar maigidan, kar ki yawaita kukan gajiya, zazzabi da sauran rashin lafiya, don in a wajen saurayi ne wata rana za ki neme shi ki rasa, ya yi tafiyarsa, in kuma maigida ne zai saba da haka ko kin zo na gaskiyan ma ba zai kula ba, zai ce ya saba da haka, in ba ki ji dadi ba ki fadi, in kin sami sauki ki ci gaba da lamuranki, wallahi akwai matan da maigida zai same su tana shewa da sauran mata, amma da ta shugo wurinsa sai ka ji ta fara cewa “Wash!” Tun ma ba in tana da juna 2 ba, babu laifi ki yi wa maigida yauki amma banda yawan raki.
Kar ki taba yarda ki sifantu da girman kai ko ki nuna wani fifiko a gaban maigidanki, ba yadda za a yi mace mai girman kai ta ce tana sane ta mamaye zuciyar maigidanta dari bisa dari, duk wace take ganin ita ‘yar manya ce a gaban mijinta, ko ba da shi take yi ba zai rika jin wani abu, in dai mace ba za ta zubar da darajarta da Allah SWT ya yi mata ba, to gwara ta dauki kanta cewa ita ba komai ba ce, namiji bankaura ne, in dai za ki yarda da cewa shi ne babba kuma sai abin da ya ce za a yi, abin da yake so shi ne dai-dai da kanki za ki gano cewa bawanki ne shi, don kusan duk abin da kike so shi ake yi, a cikin makonnan wasu suke zargin wata da shiga malamai wai ta mallake musu dan’uwa, makwabtanta kuwa da kawayenta duk sun sheda cewa da tsabar biyayyar ce ta mallake mijin.
Da yawa za ka ga wasu mata suna shakkun cewa mazansu suna kaunarsu, wata a ganinta in ta yi adon tare da yin daurin ture ka ga tsiya, gami da sanya damammun kaya, ta fitar da tsaraici don birge namijita, in har bai tanka ba to ba ta yi ba kenan, kar ki yarda wannan ya zama ma’aunin da za ki rika gwada kaunarki a wurin maigidanki. Ki waiwaya baya mana ki yi tunani, da can tun kina gidanku ba mata ne da yawa a gari? Don me ya sa duk ya tsallake su ya zo har gidanku ya dauke ki? Tabbas kin yi masa ne, ki sani wannan ma wani ma’auni ne babba da za ki iya gane cewa yana son ki. Shin matsa misha kika yi a dole sai ya zauna dake? Don bai sawwake miki ya ce ki koma gidanku ba albashi ya auro wace yake kauna ya sanya a dakin? Kenan tunda ya barki kullum ya rika hade ido dake kaunarki yake yi. Yana ciyar dake, ya tufatantar dake, ga wasu kananan abubuwa wadanda zaman aure ba ya yuwa dole sai da su duk yana sayowa, tilasta shi kika yi sai har ya kawo miki----------------?
Ga shimfidarki bai daga kafa, kullum sai ya taka, in babu kauna sam ba a ma yin wannan maganar kin ga kenan yana son abinsa. Kishinsa gare ki, na sai kin tambaye shi za ki fita, ko in kin dawo ya san halin da kike ciki, damuwarsa da lamarinki kauna ce ta zahiri. Kila ma yana da yara tare da ke, kuma bai hana ki haihuwa ba, yana kuma lalubar shimfidarsa a kowani lokaci, wanda bai cin kaza ko romonta aka ba shi ba zai sha ba, zai dauki ‘ya’yansa ya yi musu wasa, ya sayo musu ‘yan abubuwan duk da suke bukata, don haka in ba al’adarsa ba ce ya rika ce miki ina kaunarki don kwalliyar da kika yi kar ki matsa masa, akwai wasu abubuwa da dama da suke maye makwafin wannan lafazin. Daga karshe ina bawa uwargida shawara ta san irin zaman da ya kamata ki yi da maigidanti, domin kaki je fa igiyar aurenki cikin matsala.

No comments:

Post a Comment