DALILAN DAKE HADDASA MATSALAR RASHIN KARFIN MAZAKUTA



Kwalwar ‘dan adam itace babbar na’ura dake tafiyarda mafi yawancin ayyuka da jikin mutum kanyi - itace ke sarrafa duk kanin gabobi da sassan jikin mutum, kama daga tunani, ido, kunne, baki, hanci, kyaftawa, numfashi, magana, tafiya, taimakon mutum wajen harda da sauransu. Allah (S.W.A.) ya karrama ‘dan adam da kuma halittarsa. Kwalwar mutum tafi sauran kwalwar halittu dake bayan kasa dangane da tsarin halittarta, basira da yawan ayyukanta masu ban-mamaki a rayuwar ‘dan adam. Kwalwar mutum anyi wayarin nata da wasu wayoyin sadarwa masu yawa (nerves) zuwa duk kanin sassan jiki. Wadannan wayoyi suna da amfani na daban-daban. Su wadannan wayoyin sadarwa (nerves) sun lullube duk kanin jikin mutum dun daga tushensu akai (kwalwa) har zuwa kafafuwa. Amfanin wadannan wayoyin sadarwa ga kwalwa shine – daukar sakonni daga kwalwa zuwa sassan jiki ko gabobi. Misali, idan mutum yayi niyyar yin magana, kwalwarsa zata bada sakon umarni ta hanyar wayoyin sadarwar zuga gabobin jiki masu sarrafa sautin magana (su huhu, harshe, hakora, lebba da sauransu). Daga nan sai subi umarni sai baki ya furta abunda ake bukata, wanda dama can kwalwa ta riga ta yanke shawara akan abunda bakin ya fada. Da wannan hanyoyin sadarwa kwalwa ke mallakar dukkan sassan jiki wajen sarrafasu.


Haka ma, sha’awar mutum namiji ko mace na farawane daga kwalwa. Anan zamuyi bayani akan ‘dabi’ar namiji kadai. A lokacinda mutum namiji ya fuskanci iyalinsa ko wani abu na iyalinsa ya tsokano sha’awarsa ga abunda ke faruwa: kwalwa zata aika da sako zuwa hanyoyin sadarwarta dake wajen al’aurar mutum - cewa jijiyoyin al’aura su saki jiki su kumbura ta yanda za’a iya aiko da jini ya shiga cikin al’aura. Dazaran hakan ya faru, sai a harbo jini da karfi ta yanda jijiyoyin mazakutar mutum zasu kumbura (sai mazakutar mutum ta mike). Daman dai ita al’aurar namiji jijiyoyine da tsoka. Yanayin tsokar kan al’aurar yayi kama da soso. Jinin da aka harbo na cika wannan sosan tsokar da jijiyoyi sa’annan sai a kulle jinin har zuwa wani lokaci ko kuma zuwa lokacinda mutum ya biya bukatar jima’i.


DALILAN DAKE HADDASA MATSALAR RASHIN KARFIN MAZAKUTA
(CAUSES OF ERECTILE DYSFUNCTION)

Rashin karfin mazakuta na nufin matsalar rashin cikakken karfin al’aurar namiji ko raguwar karfin al’aura yayinda aka fara saduwa ko kuma rashin mikewar al’aura yayinda ake bukatar fara jima’i. Bincike ya nuna cewa wannan matsala tafi yawa ga masu shekaru 40 zuwa 70, kuma tana karuwane a lokacinda mutum yake manyanta. Saidai duk da haka akwai matasa da dama masu irin wannan matsala. Wasu daga cikin dalilan wannnan matsalar sune kamar haka:

1. Ciwon suga, hawan jini da yawan kolesterol a cikin jini (diabetes, high blood pressure and high cholesterol). Irin wadannan matsalolin zagayawar jini a jiki da danginsu (blood circulatory problems) sune matsoli na farko masu haddasa rashin karfin mazakutar namiji
ga mutane da dama.


2. Ciwon daji (cancer) na iya yima jijiyoyin jini ko hanyoyin sadarwar kwalwa illa, wanda wadannan hanyoyi suke taimakawa wajen mikewar gaba kamar yanda muka yi bayani a
baya.


3. Hadari (accident) wanda ka iya shafar sashen al’aura ko wani bangaren kwalwa mai taimakawa wajen mikewar al’aura.


4. Yawan damuwa akan matsalolinda suka faru da mutum na rayuwa da kadaici (depression).

5. Shan sigari (smoking). Taba ko sigari na cunkushe hanyoyin jini. Tana iya sanya karancin zuwan jini ga al’aura, daga nan sai asamu rashin karfin gaba.

6. Shan giya da kwayoyi (alcoholism and drugs). Matsalar yawan shan-giya na iya haddasa rashin karfin namiji koda kau mutum bai sha giyarba lokacin jima’i, domin kuwa tana zama cikin jini. Haka kuma, shaye-shayen kwayoyi don maye da wasu nau’in kwayoyi da akeba mararsa lafiya a asibiti (their side effects), kamar kwayoyin maganin ciwon daji (anti-cancer medications).

7. Rashin kwanciyar hankali ko fargaba yayin jima’i (anxiety). Idan mutum yana tunanin cewa bazai iya biyama iyalinsa bukatar jima’i ba (misali sabuwar amaryarsa ) saboda wata matsala da yake fargaba, ko kuma yana tunanin cewa baya gamsar dasu, toh yana iya jefa kansa cikin wani halin fargaba da zaisa ya rasa karfin gaba lokacin saduwa.

8. Karancin sha’awa wanda kai tsaye nada alaka da rashin cikakkiyar lafiyar mutum.

9. Karancin sha’awar saduwa da wata macen cikin matan maigida. Hakan na faruwa idan matar batasan yanda zata jawo hankalin maigidan taba wajen kwanciya. Wannan dalili na haddasa matsalar rashin karfi. Wasu dalilan kuma nada alaka da maigidan kan bukatarsa. Shiyasa wasu mazajen ke kara aure.


10. Yawan Kiba (obesity) na hana maza karfin mazakuta, kuzari da kuma haddasa kankancewar al’aura. Da sauransu.
Related image

Idan mutum yasan yanada daya daga cikin wadannan matsaloli, toh yakamata ya garzaya asibiti da wuri domin neman lafiya da kuma shawarwarin likita.
Haka kuma yanada matukar muhimmanci mutum ya guji magungunan karfin namiji nakan hanya barkatai. Zamu bayyana abinci na ‘yayan itatuwa, ganye da shawarwari da zasu taimakama masu wannan matsala, nan gaba, insha Allahu. Idan matsalar tayi girma toh mutum ya tafi asibiti kawai dan shawo kan matsalar da wuri. Allah yataimaka. Ameen

No comments:

Post a Comment