Kayan Hana Yin Kishiya Ko Ko Kayan Fadar Kishiya?


Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata mun tattauna ne a kan abaiban dake kawo cikas a aure, wato abubuwan da suke hana yin wannan auren, musamman a mataki na auren fari. Abin da ba mu tabo ba a wannan bangare shi ne ire-iren wadannan matsaloli ga mutumin da zai kara aure, wato yana da aure, mace daya ko biyu ko uku, kuma sai yake son yin kari. Misali, idan mace daya ce da mutum, to yayin da zai yi kari, nan ma wani tashin hankali ne bayan na kishi; akwai batun yi wa uwargida kaya kwatan-kwacin na amarya, ko kasa da shi kadan.

Kamar yadda muka sani, lefe wata al’ada ce dake gudana a yayin da mutum zai yi aure, al’ada ce dadadda wacce bincike na ya kasa gano mini asalinta.

Al’adar ba ta tsaya ga mutumin da zai yi aure fari ba, ta shafi hatta wanda zai kara aure ko wanda zai auri bazawara, sai dai ya danganta da yanayin guri da wacce za a aura.

A lokacin da mutum zai ‘kara aure, kusan wajibi ne ya sayowa uwargida kayan lefe wanda ake kira kayan fadar kishiya, kuma idan son samu ne ya sayo mata dukkanin irin abin da ya sayawa amaryar da zai auro. Wasu na kallon hakan ne hanya da za ta kwantarwa da uwagida hankali a game da kishiyar da za a kawo mata, a ya yin da wasu ke ganin kyautatawa ce ga uwargidan kasancewar an dad’e ana tare.

Abin da yawan mutane ba su fahimta ba, shi ne wannan al’adar na daga cikin abubuwan dake kawo tsaiko wajen yawaitar kara aure a tsakanin al’umma. Na tabbata da yawa cikin magidanta na da burin kara aure domin a rage yawan adadin mata akan tituna tare da samar musu nutsuwa da kwanciyar hankali. Da a ce al’umma za ta fahimci wannan al’ada, ta yi mata kallon nutsuwa da fahimta yadda yakamata, da ta gamsu da abinda nake zayyano.

Tunanin wasu magidanta ko matsalarsu, ba ta sauran kayan masarufin yau da gobe ba ne, a’a, tunaninsu makudan kudaden da za a kashe wajen hada wadannan kayan, har ma ya kasance auren fari shi ne ya fi dadi da sauki ga matasa sama da a ce za su yi kari.

Hakika idan ka bibiyi al’umma a yau, burace-burace ya yi musu kaka-gidan da ya kawo babban tsaiko ga rayuwarsu, ya ruguza zamantakewar gidaddajinsu, wanda idan aka dubi al’ummarmu ta jiya; ba haka wannan abu yake ba, domin akwai tsari da manufa sabanin yau. A yau, al’ummarmu ta tagayyara kanta sakamakon riko da wadansu bakin al’adu munana. Idan muka kalli yawaitar mata a tsakanin al’umma, za mu ga wani babban alami ne dake bayyana mana yadda al’ummarmu ta gigice ta dimauce. Da za ka samu damar tattaunawa da mata goma, a muhallai daban-daban, to fa kowacce cikinsu za ta bayyana maka takaicinta na rashin aure, za kuma ta nuna damuwar son miji idan ba ta fa aure, idan kuma tana da shi, to tunaninta ya za ta aurar da yarta ko ‘ya’yanta mata. A nan, ita ta yarda ta dauki ‘yarta ta kai ta tsakankanin kishiyoyi, amma ba ta yarda ita a kawo mata kishiya ba! Wane irin rashin adalci ne wannan?

A takaice dai, abubuwan da muka zayyana a satin da ya gabata, da irin abubuwan da yau muka dan yi tsokacinsu, abubuwa ne dake kawo cikas a harkar auratayya, ko dai su zama sababin haramta auren, wato su hana a yi auren, ko kuma su zama sababi na rashin kwanciyar hankali a gidan auren. Domin duk uwargidan da ba a yi wa kayan fadar kishiya ba, to za ta iya haifar da babbar matsala a yayin auren.

Babu laifi ga magidancin da zai kara aure ya yi wa uwargidansa kaya daidai gwargwado, amma kayyadewa da matan ke yi; har ta kai ga ana tayar da zaune tsaye, wannan shi ne matsala. Sannan wani abin lura, uwa da makarbiya da dangin ita uwargidan ke yi wajen ganin lalle sai an yi mata duk abin da aka yi wa amarya. Irin wannan takurawa maras dalili, idan ba Allah ba ne ya kiyaye, sai ka iske miji ya saki uwargidan kuma ya auro amarya, kun ga kenan an yi ba a yi ba. Idan da al’umma za ta fahimci abin da yake na wajabci da kuma kyautatawa, to da tuni an bar wannan layin, da an samu kwanciyar hankali a tsakanin ma’aurata.

Wata matsala da ya kamata mu kai ga hangenmu ita ce, auren nan fa ana yi, ana rage yawan matekun da suke layi. A gefe guda kuma, saki ma kara yawaita yake yi, har ma wasu masu hasashe ke ganin mutuwar aure a yau; ta fi daura shi. A wani lokaci kuwa, sai ka nemi gaskata wannan batu, domin inda kamar yadda ake daura aure haka ake yi ga rabuwarsa, kusan sai ka ga an yi kunnen doki. A yau, kusan kullum ma sai an yi saki, sati biyu zuwa wata guda da daura aure, sai ka ji an ce ya mutu. Sannan mafi yawan mace-macen auren nan fa, yana da alaka da wadancan tsadar da tsarabe-tsarabe na babu gaira babu dalili da al’umma ta matsanta wa kanta a kai.

Bisa haka a karshen wadannan batutuwa nawa nake kira ga al’umma da su tausasa wa junansu, aure albarka ake nema wadda za ta haifar da kyakkyawan zaman lafiya tsakanin ma’aurata da kuma al’umma ko dangi gaba daya. Don haka, ku yi abin da za su iya cikin kyautatawa ba tare da an matsanta ba. Da fatan Allah ya taimake mu, Ya azurta mu daga zuri’a mai aminci da zaman lafiya, amin.

No comments:

Post a Comment