Yadda Zaka Fahimci Mace Na Sonka


Hikimomin Gane Idan Ana Sonka:========

Idan kana son ka gane da gaske ana sonka,
wadannan sune alamomin.

Wannan rubutu yana
da dangantaka ne da duk wanda yake tantamar
soyayyar da ake masa, ta haka ne zai gane, duk
da cewa dai soyayya ta gaskiya ba a gane ta a
lokaci kankani kasancewar tana shiga ne sannu a
hankali. Ita soyayyar gaskiya tana toho ne da
yaduwa a cikin zukatan mutane a yayin da ake
zama ana fahimtar juna. Wani abin bakin cikin
yanzu shine soyayyar gaskiya ba ta cika dorewa
ba. Wani lokacin sai an yi nisa sai a ~ata ko ta
lalace, Wannan bayani ya gudana ne ga duk wani
masoyi da yake shakkun masoyiyarsa ko tana son
sa ko ba ta son sa.

• Idan tana yawaita fada maka tana sonka kuma
ka tabbatar da hakan, tana jin son sosai a
zuciyarta, sannan kuma tana jin son ba tare da
tana rokonka wani abu ba, sakamakon hakan ba
ta jin bacin rai kuma ba ta bata maka rai.

• Idan tana magana ka rinka kula da idonta,
wajen magana za ka iya gane mace in tana sonka
idonta yana nuna alamun tausayi da soyayya ga
wanda take so da kauna. Duk ta kwayar idonta
za ka iya gane mace in mayaudariya ce ko
dabara da wayo take maka. Shi ya sa aka ce abu
mafi sauki da muhimmanci ka rinka kula da
kwayar idonta wajen fahimtar son da take maka
in dai tana matukar sonka za ka gani.

• Za ta rinka yin duk wani abu da ta san zai
faranta maka rai. Mata suna nuna kulawa sosai
ga wanda suka damu da shi, shine sai a yi maka
abu ba tare da ka tambaya ba ko Ka nuna kana
so ba, in dai an san ka damu da abin saboda son
da ake maka. Za a yi don a faranta maka rai.

Wannan duk alama ce ta ana sonka.

• In tana sonka babu ruwanta da wasu samarin,
na san ba kowane zai yarda da haka ba. Amma
soyayya ta gaskiya ido rufewa yake, in dai mace
tana sonka idonta rufewa yake ba ta ganin kowa
a gabanta sai kai. Kar ma ka damu kanka a kan
da namiji saboda idan idon sun rufe babu kowa
da ya mamaye zuciyar sai kai. To ka ga kenan
tunaninta, jinta da ganinta duk naka ne.

• In tana matukar sonka za ta yi kokarin ta ga ta
magance duk wata damuwa da ta shafe ka, da
duk matsalar da ta dame ka za ta rinka jin duk
wata damuwa taka kamar tata. Saboda haka idan
dai har mace tana daukar damuwar wanda take
tare da shi kamar yadda za ta dauki tata
damuwar to a gaskiya wannan ita ma alama ce
ta tana sonka kuma tana tare da kai.

• In tana sonka za ta rinka tinkaho da alfahari da
samunka, da kuma nunaka a gurin ’yan’uwa da
abokan arziki, kawaye da sauran su. Saboda in
mace tana sonka gani take ka zama wani
bangare na jikinta. Wannan ne zai sa ta rinka
tinkaho da kai ba tare da jin nauyi ko kunya ba.

• In tana sonka za ta rinka fifitaka a kan ko wane
abu, idan ma tana tare da wasu da suke tare da
ita ka shigo kuma ta ji ta fi sonka to za ta fi
fifitaka a kansu kuma za ka gane, saboda za ta fi
son ta ga tana tare da kai ba tare da gajiyawa ba,
da son yin waya da kai ba gajiyawa, sannan za
ta rinka goya maka baya da nuna maka soyayya
a kan za ta iya rabuwa da kowa saboda kai.

• Damuwa da kulawa da kai a duk lokacin da take
tare da kai, mata suna son su rinka kula da
wanda suke masa son gaskiya a cikin dadi ko
rashin dadi, ko da lafiya ko babu lafiya kuma ba
tare da nuna damuwa ko bacin rai ba. Wadannan
alamomi sun isa su nuna maka mace tana sonka
kuma tana tare da kai.

• Idan tana sonka za ta yawaita tambayar
’ya’uwanka da abokanka sannan za ta rinka
girmamaka da duk wani abu da ka ke so, ba za
ta so bata maka akan abin da ta san ka dauke
shi da muhimmanci a rayuwarka ba. Misali
’yan’uwa da harkar kudi da harkar jin dadi,
addininka da dai duk wani abu da ta san ya
kunshi al’amurran rayuwarka. Irin abubuwan da
ta san kana so, kamar in kana son barcin rana in
matar ka ce ba za ta tasheka ba, don ita ma tana
son duk wani abu da zai ba ka jin dadi.

5 comments:

  1. Gaskiyane wannan abinda kuka lissafo,kuma a gaskiya sae yanxu na gamsu Dari bisa Dari cewa soyayar dake tsakanina da budirwata da gaske take sona

    ReplyDelete
  2. Rubutun ya bada ilimi sosai. Sannu da kokari. Allah ya biya

    ReplyDelete
  3. Rubutun ya bada ilimi sosai. Sannu da kokari. Allah ya biya

    ReplyDelete
  4. Rubutun ya bada ilimi sosai. Sannu da kokari. Allah ya biya

    ReplyDelete
  5. Rubutun ya bada ilimi sosai. Sannu da kokari. Allah ya biya

    ReplyDelete