Ababai dake kawo rashin jin Dadin Aure


Yar uwa idan kinason kiji dadin aure ki dena kallon rayuwar gidan wasu, kece zaki sauko kasa daidai da karfin mijinki ku gina rayuwa bisa gaskya da amana. Babban makamin ribace mu shine ki kokarin sanin bukatun mu wato (NEEDS) Inkika san wannan kika cire kasala kika kula dasu, koma kurum ki kwanta kin mallake mugun kingama komi girman kansa
Karkice komi sai kinjira yai magana, kema rika fadamasa cewa wane ina kaunarka, hasali ma kike fadamasa wannan kalmar fiye da yadda shi yake fadamiki. Ina sonka tare da kaunarka fiye da komi koda hakan zai zamo karshen numfashina, duk sanda na bude ido na ganmu tare nakanji na kara samun nutsuwa, ko bani lfy naji ka dafa ni kaimun murmushi tun kafin kai mun addu'a na kanji sauki ya fara samuwa. Damuwarka - damuwata ce my King, dade sauran kalamai komi talaucin mijinki kuwa, kike farautar maganganu, sannan ki lura da tsafta saboda namiji ko baida cikakkiyar tsafta yakanso mace mai tsafta.

SAI SAURAN TRICKS DIN DON INGANTA ZAMANTAKEWAR

➡Kina son mijinki kar yai sha'awar wata ?
Toh zamo mai tsafta kamar yadda nace.
➡Kina son kada mijinki yake yin zina ?
Ki kusance shi, ki zamto tare dashi ko yaushe, karkike jiran sai shi ya nemeki shimfarda ko yaushe
➡Kina son hira da mijinki ?
Ki zamo mai auna magana kafin ta fito, tare da tanazar sabon mau'du'i kullum
➡Kina son kyauta daga mijinki ?
Ki yawaita godiya agaresa adukkan abunda ya kawo ya baki.

➡Kina son mijinki ya aminta dake ?
Kar kike yi mishi sata, kar ki yawaita roko, da dora lalura mai nauyi da kikasan ba dole bace a kansa.

➡Kina son mijinki ya rika yi miki fara'a ?
Ki kiyayi aikata abunda baya so.

➡Kina son mijinki yake hadawa da kunyarki ?
Ki zamo mai hakuri, ladabi da nutsuwa

➡Kina so mijinki yaga girmanki ?
Ki zamo mai rike sirrinsa, mai kwantar masa da hankali yayin da ya shiga damuwa, haka zalika ki zamo mai nuna kunya wasu lokutan

➡Kina son mijinki ya rika yabonki ?
Kar ki zama mai roko akoda yaushe, tare da fadamasa cewa ai mijin wane kaza yake mata shi.

➡Kina son mijinki ya zama mai gaskiya a gareki ?
Kada ki yaudareshi, kike rike sirrinsa, ki sani mijinki rabin jikinki ne don haka kyautata zama a tsakanin ku shine rahama da jin dadi a tsakanin ku.

Mata Aure da maza amana ne a gareku, kamar yadda kuke amana a garemu.
Yan fis-fis zasuce Dr. Komi da ruwansa, yanzu kuma ya koma gyaran aure. Toh aishima wannan kula da lafiya ne, domin yaran da aka saki iyayen su sukan shiga halin lalacewar da marayu ma wadanda iyayensu suka mutu basa shiga, duk wacce zakaga ta lalace, batajin magana, ko anyima fyade inka duba da yawa xaka tarar ansaki mahaifiyarta bata gidan

Aurene kadai halattacciyar hanyar karuwar yawan jama'a a duniya, inta sami matsala ya'yan banza ne zasu cika duniya su addabi kowa kamar yadda aketa wai wai yanzu. So muke kowa sha'awa abun ya kamasa ta yadda za'a kange 6arna
Allah ka karama rayuwara aure albarka, ka kau da dukkan sharri, ka hada kowa da abokan xama nagari amin

No comments:

Post a Comment