Maganin Zubewar Gashi ga Mata



Alhamdulillah barkan mu da sake kasancewa tare da ku,a yau cikin nufin Allah zamu kawo muku bayani game da yadda za'a magance matsalar zubar gashi ga mace ko namiji.

Kuma wannan hanya bawai iya zubar gashi take magancewa ba harda amosanin ka da kwarkwata duk tana magance su cikin nufin Allah.

ABIN DA ZAA NEMA SUNE :
1. Apple cider vinegar (khaltuffa)
2. Coconut oil (man kwakwa)

Da farko zaka samu ruba irin ta fesa ruwa ko wani abu dai,sai ka zuba khaltuffa 1/4 na rubar sannan ka cike ta da ruwa,ka girgiza amma idan macece ta tabbatar kanta babu kitso sai a rika fesa shi a duk ko ina na kai a tabbatar ko ina da ina ya samu,sannan a samu hula(hat) ko dan kwali(kallabi) a rufe kan na tsawon minti 15 sannan a wanke da ruwa,zaa iya wankewa da sabulun wanke kai.
Bayan kan ya bushe sai a shafe shi da man kwakwar(coconut oil) haka zaa rika yi har sati 2.
INSHA Allah zaa rabu da wannan matsala.
Abin sadaqa ayiwa Annabi sallallahu Alaihi wasallam salati.

No comments:

Post a Comment