Ba za ka iya kirga adadin aurarrakin da suka mutu ba sakamakon rashin fitar jini daga gaban amaryar da angonta ya aureta a matsayin budurwar da shi zai bareta a leda A yadda muka dauka shi ne, sai ango ya ga amaryar kaca-kaca cikin jini a darensu na farko, shi ne zai tabbatar masa da cewa amaryar tasa bata taba sanin da namiji ba Ita kanta amaryar cike ta ke da fargaba na ko angon nata zai tono jini ko kuma a’a ko da kuwa ta san ba ta taba aikata lalata da wani da namiji ba kafin aure Ba sabon labari bane ba a wasu zamaninnika da suka gabata cewar har jefa amaryar a ke yi da zarar mijinta ya yi saduwar farko da ita kuma jini bai fita ta gabanta ba Har farin kyalle ake shimfidawa akan abin kwanciyar amarya da ango a darensu na farko don a tabbatar da zubar jini daga gaban amaryar, kuma cikin alfahari za a yi ta yawo da kyallen ana nunawa manya fa cewa “Wance bata zub da mutunci ba kafin ta yi aure” Wannan dabi’a ta fitar jini daga farjin mace a jima’inta na farko ba mu kadai ke da ita ba. Mutanen Pakistan, Indiya, Bangladesh, Afghanistan da sauran kasashe na da irin wannan tunani na cewa dole sai jini ya fita daga gaban mace a jima’inta na farko.
Kuma idan har ta sadu da namiji a matsayin saduwar farko, kuma bai ga jini ba, to lalle ta taba saduwa da wani kafin shi kuma a wancan saduwar tata, jini ya fita Wannan batu namu ya zo ne da nufin karyata wancan tunani da ke cewa wajibi ne macen da ba ta taba saduwa da da namiji ba ta fitar jini ta gabanta a yayin saduwarta da da namiji a karo na farko.
Wannan ko kusa ko alama ba gaskiya bane. Batun shi ne, ba kowace mace ce ke fitar da jini a lokacin da namiji ya kawar mata da budurcinta ba, Wasu na fitarwa, wasu kuma basa fitarwa, kuma hakan ba ya na nufin lalle ba wankakkun ‘yan mata bane don basu fitar ba Domin fahimtar dalilin da ya sanya wasu mata ke fitar da jini wasu kuma akasin haka a jima’insu na fari, ya kamata mu fahimci cewa akwai wata fata ko tantani maras kwari da ke rufe farjin mace tun daga haihuwarta. Fatar ba wai tana rufe kafatanin farjin mace bane.
Hasali ma dai, ba kasafai a ke samun macen da farjinta ke lullube da tantanin budurci ba Wani abu da ya kamata mu kara fahimta a nan shi ne, ba dukkanin mace ba ce ke da wannan tattani na budurci a lullube a gaban farjinta.
A yayin da, kamar yadda hoto na sama ya gwada, wasu mata ke dauke da fatar a lullube da gabansu, wasu ‘yar kadan ce, wasu rabin farjinsu, wasu kaso biyu bisa uka da dai sauransu.
A saboda haka, mace mai tantanin budurci mai kauri (wanda ya lullube gabanta gaba daya) dole za ta fitar da jini a yayin jima’inta na farko sakamakon sai namiji ya fasa wannan tantani kafin ya samu samu shiga Ita kuma mace mai matsakaicin tantani, dole jinin da za fitar ba zai kai na wancan ta farko ba. Haka abin zai kasance har zuwa kan wacce sam ba ta da tantanin budurci.
Ita wacce ba ta da wannan tantani, ba ta fitar da jini ko a jima’inta na farko Ga yawancin mata, wannan tantani na ficewa da kansa sakamakon yin abubuwa na motsa jiki kamarsu tukin keke, sukuwa a kan doki, wata ma daga yin rawa ko kuma ta hanyar yin amfani da kyalle a maimakon auduga a yayin al’ada. Wannan na faruwa ga mace da ke dauke da tantanin budurci maras kwari Yana da kyau mu fahimci cewa, tantanin budurci na shafewa da kansa bisa dalilin girman mace. Anan muna nufin, mace mai karancin shekaru (kamar shekaru 16 ko kasa da haka) na da yiwuwar fitar da jini a jima’i na farko sama da ‘yar shekaru 25 zuwa sama Ya kamata maza su fahimci cewa, sau tari ba ma tsagewar tantanin budurci ke haifar da jinin da mace ke fitarwa a lokacin jima’inta na farko ba, a’a, wasu mazan kan gaza yin hakuri ne su bi matan a sannu a hankali ta yadda za su shiga matan har su kai ga yi musu raunin a gabansu wanda shi ne a lokuta da dama ke haifar da fitar jini Da a ce maza da dama na fara yin wasa da mace na tsawon lokaci ta yadda har sai ta kamu ko ta bukatu, da da dama ba a za ga fitar jini ba a gaban mace ko dai ta hanyar yi mata rauni ko ta hanyar fasa tantanin budurci A takaice dai, babu wata hanya takamaimai da mutum zai iya tabbatar da cikar budurcin mace ko akasin haka. Fitar jini ba hujja ba ce, saboda fitar jini ya danganta ne ga irin tantanin budurcin da mace ke dauke da shi tun daga lokacin da aka haifeta.
Akalla, kaso 63 na matan duniya ba za su fitar da jini ba a lokacin jima’insu na farko.
Kaso 37 ne bisa hasashe za su fitar da jini a lokacin jima’insu na farko bisa bincike mai inganci da aka wallafa a wata mujallar lafiya ta kasar Ingila Samun ilimin budurci na da matukar alfanu ga maza da mata, musamman ma maza. An zargi mata, an wulakantasu, an ci zarafinsu, aurensu ya mutu, a shekaru da dama da suka gabata ma an jefe mata kawi don ba su fitar da jini ba a lokacin jima’insu na farko.
Wannan ilimi ko shakka babu zai taimaka wajen kare mutunci da muhibbar mata, tare da fitar da su daga zargin mazajen aurensu, iyayen da danginsu Mu kiyaye, ba duk wacce bata fitar da jini a daren farkonta ba ce, wacce ba ta da budurci.
Don Allah Ataimaka a yada don al’ummata ta amfana.
No comments:
Post a Comment