Hujjar su anan ita ce, sunyi
saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu
ga jini ya fito ba..
Gaskiya wannan ba hujja bace da za'a yi wa
mace kallon 'yar Iska.
BUDURCI:- Wata fata ce dake cikin farjin mace
matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan
tana yagewa ne da zarar ta samu takura.
Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan
hanyoyin..
1. Saduwa da namiji
2. Daukar kaya mai nauyi
3. Guje-guje
4. Hawan keke
5. Hawan doki ko jaki
6. Mummunar faduwa
7. Sanya danyatsa a farji
8. Haihuwa..
Wasu matan ko an sadu dasu
fatar budurcinsu bata yagewa
har sai sun zo wajen haihuwa ananne zata yage.
Dan haka nake kira ga samari
don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar
yace lallai sai ya ga wannan jinin*****
Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa
matarka kallon'yar iska ko mazinaciya domin
inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun
kafin kuyi Auren, azatona tunda sanda kayi
bincike kamin kayi Auren,domin ba'a zama da
zargi don da zarar Zargi Yafara shiga Aure To aure zai lalace.
Allah ya kiyaye mu da kiyayewarsa Kuma Allah
yasa 'yan uwana maza su Fahimta, Allah ya bamu Yaya na gari tare da Zuriya daiyiba.
Aameen....
No comments:
Post a Comment