Wani dan Izala mai suna Ahmad Abdullahi Assaminaky, ya koma Shi’a a Najeriya.
Ahmad, wanda dan kungiyar Izala ne a baya ya wallafa wannan bayani ne yau a shafin sa na Facebook, inda yace;===
“DAGA YAU NA KOMA DAN SHI'A MABIYIN ZAZZAKY
Wallahi na dade ina nazarin shin anya malaman mu na Izala a kan gaskiya suke kuwa? saboda a duk malaman kasar nan kai haddama duniya gaba daya a iskar nan ta yau dake juyawa babu wani malami da yake damabiya kuma mabiyan na shi har su rika mutuwa saboda kare rayuwar shi sai Zakzaki.”
“Kai ko annabi ne daga cikin Annabawa aka kashe mutum sama da dubu saboda kare rayuwar shi kafin akai kan shi abin a jin-jina ne balle malami,
wannan abubuwa sun sani tinanin anya wannan mutun ba mujaddadi ba ne kuwa ? domin ko asiri yakewa mabiyan nan na shi asirin yakai asiri, ni dai duk dadewar da nayi ina Ahlussunna ban tabajin za'azo kashe wani malamin Izala inji cewa zan iya bada rayuwa ta dan in kare shi ba, dubi girman malam Ja’afar wallahi masallacin nan duk tserewa akai lokacin da akaji ana harbin shi.”
“Kai gaskiya in ba wata sika daga ubangiji ba, ba zai yiwu wannan malamin ya ban-banta da sauran malamai ba shin wai waye malam Zakzaki ne.” Inji Ahmad Abdullahi Assaminaky.
No comments:
Post a Comment