Dokar Daidaita Tsarin Rabon Gado Tsakanin Maza Da Mata A Nigeria


Mai Alfarma Sarkin Musulmin Nigeria Khadimul Islam ya mayar da zazzafan raddi game da batun dokar daidaita tsarin rabon gado a Nigeria tsakanin maza da mata da ake kokarin tabbatarwa nan ba da jimawa ba
Sarkin Musulmi yace har abada Musulmai ba zasu bi wannan dokar ba, ba za'a mata biyayya ba, hukunci da dokar Musulunci zamu bi
Akwai wata 'yar boko aqeedah fitsararriya 'yar iska wai 'yar gwagwarmaya da take kare hakkin da 'yancin mata, itace ta gabatar da wannan kuduri na doka, a nufinta Musulunci ya tauyewa iyaye mata hakkinsu na rabon gado, don haka a daidaita rabon gadon.
Batun rabon gado Allah Madaukakin Sarki da kanshi Ya yi bayani a Qur'ani cewa ga yadda za'a raba, don haka babu wanda yake da karfin ikon tilastamu mu kaucewa wannan doka na Allah Madaukakin Sarki, don haka sako ya kai garesu cewa mu Musulmai tun kafin a tabbatar da dokar mun karyata ba zamuyi biyayya ba
Hikimar da ya sa Allah (T) Ya fifita rabon gadon maza a kan na mata shine; ita mace duk inda take a duniya tana karkashin ikon kulawar namiji ne, cinta da shanta da tufafinta da ilminta da komai nata an daurawa namiji, saboda tausayawa da adalci da kiyaye mutunci irin na Musulunci ga iyaye mata dangin rauni
A yau Mahaifi ya kwanta ya mutu ya bar 'ya'yansa magada maza da mata, to matan zasu koma karkashin kulawar yayunsu maza ne, gadon da aka barwa mazan shi matan zasuci, su kuma matan nasu kason gadon sun tanadashi, ashe Allah baiyi hikima da adalci anan ba da Ya fifita gadon maza a kan na mata?
Su mutanen banza 'yan Boko aqeedah suna da kwakwalwa amma tunani irin na dabbobi suke da shi, karshen rashin kunya kenan da fitsara da rashin albarka wani katon banza ko katuwar banza suce zasu ci gyaran Allah Madaukakin Sarki
Yaa Allah Kar ka kamamu da laifin da wawayen cikinmu suke aikatawa, idan Ka tashi saukar da bala'i ya kare a kansu su kadai

No comments:

Post a Comment