YA DAURA DAMARAR LALATA TARBIYYAN 'YAN MATA MUSULMAI
Daga Datti Assalafiy
Jama'a kwanaki Adam A Zango ya fitar muku da sanarwa yace ya fice daga kungiyar Kannywood saboda wai an kama abokinsa daraktan shirya fina finai OSCAR, yanzu yana so zaici gashin kanshi, tun daga ranar da ya bayyana ficewar mun san dalilin da yasa yayi hakan
Babban dalilin da yasa Adam A Zango ya fice daga Kannywood ba don an kama OSCAR bane, dalilin shine ya tanadi wasu shirye shirye na iskanci da badala a cikin film da waka da rawa na fitsara da rashin albarka, yana so ya fitar da su kasuwa, amma tsoron kamun hukumar tace finafinai na jihar Kano ya hanashi fitarwa
To shine bayan an kama OSCAR sai yayi amfani da wannan damar yace ya fita daga cikin kungiyar Kannywood don ya samu ikon yada fasadi da barna a tsakanin Musulmi, Billahi munyi wannan binciken har daga abokan harkansa na kusa da suka san sirrinsa ciki da bai
Muna kan nazari a haka, kwatsam sai dazu mukaci karo da sanarwan da Adam A Zango ya fitar cikin bidiyo a shafinsa na Instagram yana mai cewa; yana neman 'yan mata kyawawa danyu shakaf wadanda suke tashen balaga 'yan kasa da shekarun haihuwa 18, yana so zai sakasu a film, sai ya saka wani link, yace duk wacce take bukata ta saka hotonta da dukkan bayananta
A ka'idah wannan tsarin da Adam A Zango ya fitar ya karya kowace irin doka na shirya fina finai a Kasarmu Nigeria, sannan sai muka fahimci wannan wata hanyace da yake so yabi domin ya cimma wani buri nashi, ayi kasuwanci da 'ya'yan mutane a kuma lalata musu tarbiyyah da rayuwa
Amma zamu tura 'yan leken asirinmu daga cikin irin 'yan mata da yace yana so Insha Allah, kuma hakkin gwamnatin jihar Kaduna ne ta saka ido akan abinda Adam A Zango ya ke so yayi da 'ya'yan mutane, na kusa da Maigirma gwamnan Jihar Kaduna ku tayamu isar da wannan sakon
Ke kuma 'yan mata, ki sani gurin da zaki guri ne da za'a lalata miki darajar rayuwa na har abada, mutuncinki da darajar da Allah Ya miki ya kamata ki kebanceshi ga mijinki na aure uban 'ya'yanki na halal, ki sani gurin da zakije, guri ne da za'a koya miki mummunan sana'a
Target dinsa shine, duk 'yan matan da suka cike wannan form da ya fitar ta internet suka saka hotunansu, to daya bayan daya za'a dinga kiran 'yan matan ace ke kin ci screening kizo, idan an gama da ita an lalata mata rayuwa sai a kira wata sabuwa, tunda ba abune da za'a hadu a guri daya a tantancen 'yan matan ba, ta internet ne ya fitar saboda mummunan manufarsa.
Muna kira ga iyaye su saka ido akan 'ya'yansu 'yan mata
Adam A Zango kaji tsoron Allah, Ka tuna zaka mutu watarana, ka tuna daga cikin abokan sana'arka sun mutu, kai ma fa zakaje inda suka je, akwai hisabi, ina jiye maka tsoron ranar da zakayi nadama marar amfani, idan kayi sanadiyyar lalata rayuwar wani ko wata tamkar ka lalata rayuwar al'umma ne gaba daya, haka idan kayi sanadin shiryar da wani ko wata kamar ka shiryar da al'umma gaba daya, lada ko zunubinka kenan a gurin Allah.
Idan ba zaka tuba ba, to ina mai tabbatar maka ba zakaci nasara ba, domin zamu kira al'ummar musulmi, mu saka goshin mu a kasa mu kai karanka gurin Allah Madaukakin Sarki
Ina rokon Allah Ya shiryar da kai tare da masu mummunan sana'a irin taka, idan ba zaka shiryu ba muna tawassuli da Sunayen Allah AL-HAYYU AL-QAYYUM Ya mana maganinka cikin sauki Amin
No comments:
Post a Comment