
Buhari Na Wani Shiri Na Cigaba Da Jihadi Daga Inda Dan Fodiyo Ya Tsaya A Najeriya – TY Danjuma
” Ina kira da babbar murya ga dukkanin kabilun Najeriya kudancin kasa da yankin Middle Belt da cewar su farka daga baccin da suke yi,su mance da wata magana ta zaben 2019, su mayar da hankalin su dangane da shirin da Buhari ya keyi na kokarin cigaba daga inda Dan Fodiyo ya tsaya na mamayar kasashen kabilu da kokarin musuluntar da Nijeriya, da dora Hausa/Fulani akan sauran kabilun Nijeriya da karfin tsiya”
Wadannan kalamai sun fito ne daga bakin tsohon shugaban rundunar sojin Najeriya Janar TY Danjuma, lokacin da yake maida martani cikin fushi akan yawaitar kashe kashe da ke faruwa a kasar nan tamkar ruwan dare.
TY Danjuma ya cigaba da cewar, babu mai shakka akan cewar Buhari Uba ne na kungiyar Miyyeti Allah ta kasa kungiyar da ya bayyana a matsayin ta ‘yan ta’adda, kuma suna sane da shirin Buhari na gayyato Fulani makiyaya daga kasashen ketare da saya musu makaman zamani domin kawai su karkashe Kiristocin Najeriya ko kuma duk wani mutum wanda ba kabilar Hausa/Fulani ba.
Tsohon Janar din ya koka dangane da yadda Tinubu yayi sake har Buhari yayi mishi wayo ta hanyar rarraba kawunan yarbawa, da yadda aka bar Hausa/Fulani na fantamawa yadda suke so a kasashen yarbawa cikin kwanciyar hankali, inda yace lallai idan shugabannin Yarbawa ba su farka ba za su wayi gari kasashen Yarbawa sun dawo karkashin mulkin Hausa/Fulani.
TY Danjuma ya bukaci Kiristocin Najeriya dasu tashi su nemi makamai domin kare kansu daga Hausa/Fulani, domin idan aka lura dukkanin jihohin da ake kashe kashe a Najeriya jihohi ne na Kiristoci, kamar jihohin Taraba da Binuwai da Filato da kudancin jihar Kaduna inji shi.
#Mikiya
No comments:
Post a Comment