

___¥__
Rundunar Sojan Nijeriya ta yi karin haske game da arangamar da rundunar ta yi da ‘yan Shi’a a hanyar Abuja inda ta nuna cewa mabiya Shi’a ne da ke tattaki zuwa Abuja suka fara kai farmaki kan wata tawagar soja wadda ke dauke da makamai daga Abuja zuwa Kaduna.
Rundunar Sojan ta ce, mabiya Shi’ar sun yi kokarin dibar makamai daga Motoci wanda a kan haka ne sojojin suka fara harbi ganin yadda ‘yan Shi’ar ke ta jifar su da duwatsu, lamarin da ya yi sanadiyyar raunana wasu sojoji biyu tare da farfasa gilasan motocin wasu Fararen hula.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa ‘yan shi’a uku ne suka rasa rayukansu a maimakon mutane goma kamar yadda kungiyar Shi’ar ke yayatawa.
No comments:
Post a Comment