Masana a fannin kiwo lafiya sun shawarci iyaye da suke dora yaran su da zarar an haife su a bisa nonon uwa ba tare da hada shi da komai ba. So dayawa in an haifi jariri akan yi saurin shayar da jaririn ruwa a maimakon ruwan nonon mahaifiyar shi. A wasu lokuta jama'a na ikirarin wai nonon uwar jaririn na da dotti wanda akasari ba haka ba ne.
Masana sun bayyana kadan daga cikin al'fanun shayar da jariri zallan ruwan nono yayin da aka haife shi har zuwa watanni shida. Ga wasu daga ciki:
1.) Shayar da jariri ruwan nono zalla da zaran an haife shi na taimakawa gaya wajen kare jaririn daga kamuwa da cututtuka irin su cutar kenda, tarin lala, sankarau da sauran cututtuka.
2.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na taimakawa jaririn wajen girma yadda ya kamata.
3.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na bunkasa kwakwalwan yaro.
4.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na kare uwar jaririn daga kamuwa da cutar daji ko cancer.
5.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na taimaka wa iyayen wajen rage kashe kudin siyan abincin da zasu ci.
6.) Shayar da jariri ruwan nono zalla wata dabara ce na ba da tazarar haihuwa domin yana jinkirta daukar ciki.
7.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na kuma karawa jariri karfin kashi.
8.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na kare uwa daga kamuwa da cutar suga (diabetes).
9.) Shayar da jariri ruwan nono zalla na rage kiba a jikin uwa bayan ta haihu musamman wajen maida cikin yadda yake kafin ta haihu.
akika nonon uwa shi kadai zai iya rike jariri har zuwa watanni shida tare da gadar masa duk wasu matakan girman jiki da lafiya, don haka a tsawon wannan lokacin babu bukatar shayar da shi ko ciyar da shi wani nau’in abinci.
Ya zo cikin ruwaya cewa: Imam Ja’afar Sadiq
{a.s} yana wasici ga matarsa cewa; Shayar da jariri nono daga dukkanin
bakin nono biyu yana wadatar da jariri daga ruwa da abincin da yake
bukata. Wato shayar da jariri daga bakin nono guda yana matsayin ruwan
da yake bukata ne, sannan shayar da shi daga daya bakin nonon yana
matsayin abincin da ke bukata.
Haka nan bincike
na ilimi ya tabbatar da cewa; Ruwan nonon da ke fara fitowa mai
ruwa-ruwa a lokacin da mahaifiya zata shayar da jaririnta, to wannan
nonon yana matsayin ruwan da jariri ke bukata ne kuma yana kawar masa da
kishin ruwa, sannan ruwan nonon da ke ci gaba da fitowa daga mahaifiya
mai kauri, shi ne yake matsayin abincin da jariri ke bukata a rayuwarsa
na wannan lokacin.
Haka nan farkon nonon da ke
fitowa daga kirjin uwa bayan ta haihu mai launin yalo, wannan nonon yana
dauke da wasu sinadarai masu amfani da kima kuma wannan ruwan nonon
yana matsayin riga kafi ne ga jariri domin kare shi daga nau’o’in
cututtuka, sakamakon haka mahaifa su tabbatar sun shayar da jariransu
wannan ruwan nonon.
Har ila yau nonon uwa shi
ne nau’in nonon da yafi duk wani nonon da za a shayar da jariri tsabta
saboda nono ne da zai zuka kai tsaye daga jikin uwa, sabanin nonon da za
a tatso daga dabba, ko nonon da ake sarrafawa daga kamfanoni inda a
wani lokaci wannan nonon zai iya cin karo da wata kayar cuta kafin a kai
ga shayar da jariri.
Hakika a kullum nonon uwa tsabtatacce ne
kuma sabon nono da baya tsufa, sabanin sauran nonon da ake sarrafawa
watakila akwai tsawon lokacin da ake diba masa domin yin amfani da shi,
wato da zarar ya kai wannan wa’adi to nonon ya lalace kuma zai iya zama
guba da zai cutar da lafiyar jariri.
Tabbas
wasu kwararrun likitoci a fuskar kiwon lafiya da masana harkar shari’a
suna da ra’ayin cewa; Nonon mahaifiya hakkin yaron da ta haifa ne, kuma
babu wani mutum da ke musun cewa nonon uwa yana da tasiri a fagen samar
da kwanciyar hankali da nutsuwa ga jarirai. A gefe guda kuma ‘yan jari
hujja da wasu kungiyoyin da suke riya kare hakkin mata da suka yi fice a
fagen shan jinin mata ta hanyar aikatar da su, suna yada farafagandar
karya cewa; matakin da mata ke dauka na haihuwa tare da shayar da
jariransu nono yana rusa musu rayuwa tare da ramar da su lamarin da ke
kai ga haramta wa jarirai shan nonon uwa.
Hakika
irin wadannan kungiyoyi suna kokarin ganin har yaran da suka tashi a
yammacin turai tare da amfana daga nonon mahaifansu su girman cikin
mummunan halin kadaici da firgita tamkar marassa uwa saboda rashin
amfanuwa daga jin kan uwa da kusancinta ga yaranta, sakamakon shagaltar
da ita da wasu ayyukan da zasu kawar da hankalinta daga rungumar
‘ya’yanta domin rainonsu. Haka nan mahangar irin wadannan kungiyoyi ta
rashin jin kai da tausayi tana da bam mamaki a fuskar zamantakewar
iyali. Wasu daga cikin irin wadannan kungiyoyi saboda tsabar rashin
tausayi da jin kai ga yara; suna adawa tare da yin Allah wadai da duk
wani tunanin daukar mace a matsayin mahaifiya da take dauke da dabi’ar
tausayi da jin kai, sannan suna fassara hakan a matsayin zalunci ga mace
da kokarin mai da ita saniyar ware.
Shulamith
Firestore daya daga cikin masu tsaurin ra’ayin kare hakkokin mata a kan
tubalin wuce gona da iri yana bayyana cewa; “Dole ne shafe batun daukar
mace a matsayin uwa a shafin rayuwar dan –Adam”. A mahangar Shulamith
yana ganin za a iya maye gurbin shayar da nonon uwa da bai wa jarirai
madara a gora tare da kula da tarbiyyarsu a gidajen raino.
A
gefe guda kuma mahangar addinin Musulunci yana daukar mace ce a
matsayin uwa mai muhimmanci a fagen rayuwa, saboda kasancewar mace a
matsayin uwa hakan baya nufin kakkabeta daga hakkokinta ko katangeta
daga gudanar da ayyuka da hidima a fagen rayuwar zamantakewar jama’a,
don haka nau’in halittar mace da dabi’arta wasu babbar dama ce gare ta
da zai bata sukunin samar da yara lafiyayyu kuma nagari ga al’umma. Duk
da cewa babu mai musun cewa tabbas a lokacin da mace take dauke da juna
biyu da lokacin haihuwa da kuma lokacin shayar da jaririnta da kuma
tsawon lokacin tarbiyyantar da shi tana fuskantar tarin matsaloli da
wahalhalu, amma dabi’ar kasancewarta mahaifiya da kyakkyawar alakar da
ke tsakaninta da jaririn da ta haifa hakan zasu shafe mata dukkanin
wahalhalu da matsalolin da ta fuskanta a tsawon wadancan lokuta tare da
jin yarda da aminci a zuciyarta.
Tabbas
matakin da wasu mata suke dauka a wannan zamani a sassa daban daban na
duniya na nisanta daga yaransu sakamakon ayyukan da suke gudanarwa a
wajen gida, a fili yake cewa babu wani abin da zai maye matsayin uwa
tare da zaman madadinta, saboda duk wani wajen rainon yara bai zai taba
maye gurbin uwa a fagen nuna jin kai, tausayi, rarrashi, nutsuwa da
kwantar da hankalin yaro ba. Sakamakon haka addinin Musulunci ya jaddada
matsayin uwa a fagen rainon danta domin gadar masa da nutsuwa,
kwanciyar hankali, aminci da zaman lafiyan jiki da na ruhi. Don haka
yaron da ya samu babban rabo a tsakanin al’umma shi ne wanda ya samu
cikakken kula da raino daga mahaifansa musamman karkashin kulawar uwa.
Thanks for making this topic easy with your clear explanation. Find faster tips on the profile of Candy Clicker Unblocked right now. Candy Clicker’s blend of simple gameplay and creative progression makes it a fun and engaging experience for all players.
ReplyDelete