A yau ina so zan yi magana dangane da mahimmancin sana'o'in mata wanda zai iya taimakawa wajen rage matsalolin aure na yau da kullum, kuma zai yi maganin rashin abinyi. Rashin sana’a ga mace ke sawa a yau da kullum suna yawan fadace-fadace da maigidanta wala’allah akan kudin cefane ne, kudin anko ne, ko kuwa kudin kashewa ne, musamman da yake yawa-yawancin mata akwai son ado da kwalliya da kuma son abubuwan yayi. Duba sababbin sana'o in hausawa na zamani
A wannan tsadar rayuwar ta cin abinci dakyar a haka wasu matan basu hakuri da abinda aka samu. Wannan shi ke sa wasu mata su ke rage kudin cefane, ko kuwa sai yawan bani-bani wanda basi da dadi koda ga iyayen mutum ne ballatana maigida.
Sai dai ba anan gizo ke sakar ba, wasu mazan ba su son matansu na sana’a hakan ke jawo rashin ci gaba in har mijin bamai karfi bane. Ina so yar’uwa ki sani zama ba naki bane, zamani ya wuce da zaki kwanta kina jiran komai maigida ya miki, ki tuna da wakokin mutan da na amada mai cewa:
”Ku kama sana’a mata
macen da bata sana’a aura ce
lale lale maraba dake zinariya’’
Don haka ina jawo hankalin mata akan su zage damtse akan koyon sana’o'in mata wanda zasu taimaka musu da kuma yaransu har ma da mazajensu. Ba sai kin fita ba, yanzu an samu ci gaba kina daga gida ma zaki iya yin sana’a kuma ki tallata hajarki koda ta yanar gizo ne hankalinki kwance.
Misalan kananan sana’o'i da mata za su iya yi a gida sun hada da:
Sai da katin waya
Awara
Dan malele
Zogale
Aya
Gyada
Kwakumeti
Hallaka kwabo
Tuwon madara
Gullisuwa
Fara
Carbin malam
Tsami gaye
Lalle
kitso
Har ila yau akwai kayan kulle-kulle da mata za su iya iya su sayar kamar su:=======
1. Barkono
2. Magi
3. Kanwa
4. Kuka
5. Kubewa
6. Tafarnuwa
7. Masoro
8. Kanunfari
9. Citta
10. Gyadar miya
Wadannan sune kadan daga cikin kananan sana’o'in da mata zasu iya yi daga cikin gida cikin sauki kuma sukan taimaki mata wajen magance matsalolinsu na yau da kullum.
Idan kuna tare dani zan kawo bayanai game da su da kuma sana'o'i manya.
No comments:
Post a Comment