◉ LAYYA [YANKA] ◉
Bismillahir Rahmanir Rahim: .
Lallai bayani dangane da Layya tana da fad'i sosai amma zamu taqaita a taqaice. .
◉ LAYYA: ita ce dabbar da ake yankewa domin neman yardar ALLAH daga cikin nau'o'in tumaki da Awaki da Shanu da Raquma wad'anda suka cika shekarun yin layya, kuma sun ku6uta daga kowane aibi. .
→An shard'anta yanke dabbar layya a ranar 10 ga watan Zu-lhijjah da yini biyu masu bi mashi, bayan dawowa daga sallar idi, bayan kuma Liman ya yanke. [Fawakihud-dawaniy 1/440] .
→ Sheikh Abubakar Jaza'iriy ya fad'a acikin littafinsa mai suna [Minhajul Muslim] Yace: LAYYA wata dabba ce wadda ake yankewa ranar idi domin neman yardar ALLAH, ana yin ta ne don raya sunnar Annabi Ibrahim (AS) domin ALLAH Yayi wahayi zuwa gare shi da ya yanke d'anshi Isma'eel (AS), sannan kuma ya fanshe shi da Rago, ya Yanke shi a madadinsa. Kamar Yadda yazo acikin Alqur'ani ALLAH (SWT) Yace: . ﻭَﻓَﺪَﻳْﻨَﺎﻩُ ﺑِﺬِﺑْﺢٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ .
Menene matsayin wannan LAYYA???
Sai yace: Sunnar Babanku ce Ibrahim (AS). [Minhahul Muslim] .
→ LAYYA sunnah ce ta Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) kuma Ya kwad'aitar da yinta ga Al-ummarsa kuma ya tsoratar ga barin yinta ga Wanda ya samu iko da dama. .
◉ Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: " Wanda yake da wadata, kuma bai yi Layya ba, to kada ya kusanci (Filin Sallar) Idin Mu." [Sahihul Jamii 6490] .
◉ Wasu daga cikin maganganun Magabata dangane da LAYYA: .
● "Layya sunnah ce ba wajibi bace "[Bn baaz da Bn uthaimeen] .
● "Layya ta halatta mutum da iyalansa da duk Wanda yasa (musulmi) acikin layyar tare dashi" [Bn uthaimeen] .
● "Iyalai guda layya guda ta wadatar dasu, koda mutum yana da 'ya'ya masu aiki kuma suna da aure ana basu albashi, da sharadin cewa abincinsu da abin shansu gudane; ma'ana wajen dahuwar abincin guda d'ayane, Amma idan kowanne daga cikinsu yana da wajen dahuwarsa daban to layyarsa ta sa'ba da layyar sauran" [Bn uthaimeen] .
● "Wanda zai yanka layyar shine Wanda yake d'auke da nauyin gidan; Uba ko miji ko babban d'a ko babban yaya " [Bn uthaimeen] .
● "Mace layya bata lizimceta ba, tana shigane cikin ta namiji, uba ko miji ko d'a ko d'an uwa, Amma da zatayi nufin zatayi layya tana da damar yin haka, sai ta hanu daga cire gashinta da farcenta kamar namiji " [Bn uthaimeen] .
● "Ya halatta ga macce tayi layya " Bn uthaimeen .
● "Yin layya ga mamaci tana da hali guda uku, Ga maganar Bn uthaimeen: .
→HALI NA FARKO: Mamacin da yayi wasiya cewa amai layya to sai amai a zartar da wasiyarsa. .
→ HALI NA BIYU: Rayayye yayi wa kansa layya sai yayi niyar shigar da mamacin aciki tare dashi wannan ya halatta. .
→HALI NA UKU: Mutum yayi Wa mamaci layya sai dai abinda yafi kar ayi saboda Manzon ALLAH baffansa ya mutu matar sama ta mutu amma baiyi musu layya ba. .
● "Mutum yasamu yaci bashi dan yayi layya matuqar yana saran Samun ikon biyan bashin "[Bn baaz da Bn uthaimeen] .
● "Layya da shanuwa ko raqumi ana iya yin had'aka mutum bakwai amma tunkiya ba'a had'aka acikinta " [Bn uthaimeen] .
● "Abunda yafi kada mutum yayi layya da Rago sama da d'aya" [Bn uthaimeen] .
● "Mai aikin hajji baya layya sai dai zai iya barma iyalansa kud'i don su sayi abin layya su yanka wa Kansu shi kuma yayanka hadaya a Makkah bazaiyi layya ba " [Bn uthaimeen] .
● "Ya halatta ga mai aikin hajjin da yayi nufin layya ya yankata a Makkah " [Bn baaz] .
● "Ba'a layya sai da dabbobin ni'ima rakumi shanuwa tumakai, Dole dabbar layya takai shekarun da aka iyakance ashari'a: .
→Rakumi 5 →Shanuwa 2 →Tunkiya wata6 →Akuya shekara
1 . lokacin da shari'a ta iyakance ayi yanka shine bayan sallar idi har zuwa qiran sallar magrib akwana na uku ga sallah " [Bn uthaimeen] .
"layya ba tayi har sai in dabbar ta ku'buta daga aibi [Bn uthaimeen] . Wannan a taqaice kenan daga maganganun da suka ke6anci Layya. .
Manzon ALLAH (Sallallahu Alaihi Wasallam) Yace: "Lallai ALLAH Ya hukunta kyautatawa akan komai, idan zaku yi kisa ku kyautata kisarku, idan zaku yi Yanka Ku kyautata abun yankawarku, kuma d'ayanku ya wasa wuqarsa ya hutar da abun yankawarsa." [Muslim] .
Addu'ar da ake yi idan za'a Yanka dabba: . ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻛﺒﺮ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻣﻨﻚ ﻭﻟﻚ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺗﻘﺒﻞ ﻣﻨﻲ . "BISMILLAHI WALLAHU AKBAR, ALLAHUMMA MINKA WA LAKA, ALLAHUMMA TAQABBAL MINNI." . Ma'ana: " Da sunan ALLAH, kuma ALLAH ne Mafi Girma, Ya ALLAH (wannan Dabba) daga gareka take kuma mallakar kace, Ya ALLAH ka kar6a daga gare ni." [Muslim 3/1557, Baihaqiy 9/287] . ALLAH Ya bamu iko da dama Ya kuma amsa mana dukkan Ibadun mu (Ameen)
No comments:
Post a Comment