KU YI AUREN DOMIN NEMAN KUSANCI GA ALLAH


Muyi aure domin neman karin kusanci ga ALLAH, muyi aure domin ALLAH domin tabbatar da sunnahn manzon ALLAH (S.A.W).
Kada kayi aure domin jima'i kawai, sani dai aure ba jima'i ne kawai ba, a'a zamantakewa ce da ake so ta kasance har abada, kuma ibada ce cikon rabin addinin ka, sunnah ce ta manzon ALLAH (S.A.W) nutsuwa ce kuma ni'ima ce, jima'i na ɗan wasu lokuta ne kawai shin idan sha'awar ka ta sauka shikenan, Baruwan ka da matar,


Kada kayi aure domin baka son ka rasa wannan masoyiyar ta ka, saboda kyawun ta, mulkin gidan su, ko wata surar ta ko dukiyar ta ko na iyayen ta, wannan ba shine zai tabbatar da zaman ku cikin kwanciyar hankali ba, dukiya, kyawu, mulki, surar mutum, na iya gushewa a kowanne lokaci, kai de yi auren ka domin ALLAH, zaka iya auren ta saboda abunda muka lissafa a sama amma ya zamo akwai rikon ta da addini da tarbiyya, kuma ya zama auren domin ALLAH.

Kada kayi aure kawai dan an takura ka a gida, a'a kayi aure domin neman yardar ALLAH ka nutsu ka zabi abokiyar rayuwa wacce zaku kara samun kusanci ga ALLAH, kada kayi fushi ka fusata domin an takura ka gida kaje kawai ka nemi ko wacce irin macece ka aura, a'a kayi hakuri kaci gaba da addu'a ka nemi mace irin wacce kake so amma dai ta zamo mai riko da addini da kyawawan hali, dan in kace zaka yi aure cikin fusata ne don an takura ka to zaka je ne ka nemo wacce in ba Sa'a aka ci ba, za ta dagula ka ta firgita ka kuma ta fusata ka har ka fashe, dama dai zaka bi da kacire sha'awowin zuciyar ka ka nemi mai addinin dai da annabi ya kwaɗaitar, sai ka duba mai kyawawan halayya ce ? domin ana samun mace ga addini amma ba kyawawan hali

Kada kayi aure domin "yare" kayi aure domin ALLAH a kowacce yare, wacce zaka aura in dai ta zamo mai addini mai kuma kyawawan hali, kada ka zamo mai yawan alfahari da yare.

Kada kayi aure domin kawai abokan ka sunyi aure, kaje kana ta buga_buga ko ta halin ya'ya kace sai kayi, kasani komi lokaci ne ka tsaya ka nutsu kayi addu'a, ka samu sana'a kwakkwara wacce zaka iya ɗaukar ɗawainiyar matar ka daidai gwargwado iko, kaje ka nemi mace mai addini da kyawawan hali

Kada kaje kayi aure Saboda abunda yarinyar ko matar ta karanta, saboda dan ta karanta wani abu na burgewa ko abun alfahari ba shine ke nuna zaku yi aure ku zauna lafiya ba, ba shine ke nuna nasarar aure ba, a'a ka fahimce ta sosai kuma ka aure ta saboda ALLAH da kuma addinin ta da tarbiyyar ta.

Kada kaje kayi aure domin kaga wani bikin ya burge ka, ko suturar da ango da amarya suka sanya, yan'uwa kawaye, da shagulgular bikin, don ya burge ka kawai kaje kaima kace sai kayi aure hakan kuskure ne zaka je ka afka ga halaka kayi auren ka don ALLAH domin neman karin kusanci ga ALLAH da sunnah manzon ALLAH (S.A.W), in dai shagulgular biki ne da suturun biki kullum kara kyawatawa ake ana fitar da sabbi yi auren ka bisa sunnah manzon ALLAH.

Kada kayi aure Saboda kawai ka samu yara ko don kana son yara, ko don abokan ka na da yara kayi aure domin ALLAH kuma ka roke sa ya baka ƴa'ƴa idan alkhairi ne a gare ka daga duniyar ka har zuwa lahirar ka.

Kada kayi aure domin ana matsa ma ka tsufa ka girma, kaide zamo na gari kuma mai rokon ALLAH ya baka mata ta gari, nitsu ka zaɓi mace wacce za ku tallafawa junan ku daga duniya har zuwa lahira ku shiga aljannah da yardar ALLAH.
Kada kayi aure domin kawai kai kana son harkar maganar aure da sauran su, kayi aure domin ALLAH, harkar maganar aure na ɗan wani lokaci ne.

Yi aure domin neman yardar ALLAH da kwaikwayon sunnah manzon ALLAH (S.A.W), domin cika addinin ka, da samun zuriyya ta gari idan ALLAH ya ƙaddara gare ka

No comments:

Post a Comment