Gudumuwwa da Aske gashin Gaba Keyi A wajen Jima'i


Alal hakik musulunci addini ne maifadi da kuma dadi duk wani abu naruwar musulmai yatsara musu rayuwa hatta wajan biya junansu bukata musulunci baibar musulumi kara zubeba haka awajan tsaftar jiki da tufafi,

Tabbas hadisi ya inganta a bukhari da muslim daka abu huraira Allah yakara yarda agareshi, Manzan Allah sallahu Alaihi wasallam yace: abubuwa biyar suna cikin fidra abunda Allah yadabi,antar da mutane akai,
-Kaciya,
-Aske gashin gaba,
-Cire gashin baki,
-yanke farce,
-aske gashin hammata,
wadannan abubuwa suna cikin abubuwan da Allah yadabi,antar da mutane akansau, kuma suna cikin sunnoniasu karfi yakamata ga kowanne musulmi da musulma yakula dasu sosai, kaciya sunnah akan mata da maza, malami dayawa suntafi akan wajibine, musamman akan maza , wannan sananne awajan mazhabr imamu Ahmad Allah yajikansa darahma, cewa kaciya wajibice, wasu kuma sukace sunnah ce maikarfi akan duka maza da mata,
Kuma bai kamata mutum yabar wadannan ababe suhaura kwana arba,in batare da ya aske suba, gashin gaba da hammata da kuma yanke farce, da rage gashin baki ga maza,
Saboda hadisi yatabbata acikin sahihu muslim daga Anas Allah yakara yarda agareshi, yace: Manzan Allah salallahu Alaihi wasallam yasanya mana lokacin rage gashin baki, dayanke farce, da aske gashin hammata, da kuma aske gashin gaba,
Lallai yakamata ga mumini mace da namiji, kada sukyale wadannan ababe su haura kwana arba,in, kana iya kawar dasu cikin sati ukuma ko biyu, amma dai karka haura kwana arba,in,
Sannan maganar cewa wai inkana saduwa da matarka duk gashin da yashafi nata na al,aurarku zaku samu lada goma wannan karyane babu wannan maganar a musulunci,
Saida jima,i da matarka akwai lada dunkulalle da Annabi yabamu labari cewa ma,aurata suna samu yayain dasuke jima,i danbiyawa kansu bukata kamar yadda yazo ahadisi ingantacce.

No comments:

Post a Comment